Matasa a guji rikicin siyasa
Dole ne in yi wa kaina adalci, don ba zan ci zamanina, in ci na wani ba, don haka ba zan kira kaina matashi ba. Hausawa na cewa in an girma, a san an girma, don Allah a rinka tunani. Kuma ni dai ba aiki za a daukan ba, ballantana in rage shekaruna; ba kuma […]
Dole ne in yi wa kaina adalci, don ba zan ci zamanina, in ci na wani ba, don haka ba zan kira kaina matashi ba. Hausawa na cewa in an girma, a san an girma, don Allah a rinka tunani. Kuma ni dai ba aiki za a daukan ba, ballantana in rage shekaruna; ba kuma takara zan yi ba. Allah suturi bukwai inji kishiyar mai mageduwa.
A tawa shawarar duk wanda ya dara shekara 35 ya fitar da kansa daga sahun matasa. A ganina in ya dara shakara 40 kuma yana kiran kansa matashi, bai gode wa Allah ba. Don shekaru rahama ne, idan ka samu ka zama mai godiya ga Rabis samawati.
Domin a cikin wadannan shekarun komai dakikancin mutum dole ya ilimantu da darasin yau da gobe, kuma dole akwai ilimin da ya samu na rayuwar duniya, wanda za a iya amfanuwa da shi. To na me Allah Ya yi mini baiwa da shekaru zan zama butulu? Dalilai marasa tushe kan sa ’yan sama da shekara 40 kiran kansu matasa. Ni ba matashi ba ne don na dara wa shekara 40, na yi aure, ina da shekara 23. Ina da shekara 24, na samu dana na farko.wanda ya rasu bayan watanni da haihuwarsa.
Ina da shekara 25 na haifi dana na biyu. kuma yana raye yana karatu,yana yawan cika min gida da matasa. Sai in dawo cikin abokansa, in ce ni matashi ne? Ka san rayuwarmu ba ta ’yan bariki ba ce. Don haka tun kafin in haifi dana na farko marigayi da na biyu dan matashi ina rike da yara biyu mata. Ina da shekara 23, dayansu na da shekara biyu, daya watanni tara. Wadannan yaran duk an aurar da su, suna auren wadansu matasan. Shi ke nan sai in dawo cikin surukaina, in ce ni ma matashi ne? Babu godiya a ganina, ga duk wanda ya haura 40 ya kira kansa matashi. Domin ko a Musulunci shekara 40 na daga cikin shekarun cikar hankali; ko Bature cewa ya yi wawan shekara 40, wawa ne har abada.
Daga shekara 40 zuwa 55 kamata ya yi mutum ya zama tsaka-tsakin mai bai wa matasa shawara. Daga shekara 55 zuwa 70 dattijo daga 70 zuwa sama tsoho. Allah Ya sa mu zama dattawan kirki, mu kuma yi tsufa mai kyau. Don kuwa duk matashin da bai yi rayuwar kirki ba, zai zama dattijon banza; zai kuma tsufa a wulakance, zai mutu cikin kaskanci, Allah Ya kiyaye mu.
A matsayina na mai bai wa matashi shawara, kan yadda zaben nan ya taho, zan shaida masa cewa, ‘duk wani dan sama da 40 idan ya shigo cikin wadanda ya kamata ya ba mu shawarar kirki bai ba mu ba, zan dauke shi a mutumin banza! In dattijo ne na banza, in kuma tsoho ne, wanda tsufa ya yi gardama, to ya zama tsohon banza!
Ba zan yarda da wanda zai ce in je gidan wani da muke da bambancin ra’ayi in kai farmaki ba. Domin sau da yawa irin wadannan hare-hare ana kai su ne domin hassada kawai, sai a ce bari rikicin siyasa ya barke, gidan wane da wane sai mun kona su. Matasa su sani mafi yawa daga cikin hankoron taba dukiyar wani hassada ce kan kawo su, kuma ba wani amfani wannan zai yi a nuna fushin zabe ba. Wane ne zai iya canza wannan? Da ina cikin matasa ba zan bari a yi amfani da ni a kone-kone domin zabe ba.
Da ina cikin Matasa ba zan bari a yi amfani da ni wajen kona kayan gwamnati ba. Don kuwa kayan gwamanti kayanmu ne, kuma kaso na kudin kasa, wanda ina da kaso a ciki, don haka ba zan kona ba, ba zan bari a kona ba.
Dole matashi ya san mulki canjawa yake, amma kayan gwamnati suna nan. Idan mai mulki ya tafi dole ya bar aikin da ya yi. Ya yi kadan ya kai gidansu ko dakinsa. Don haka amfaninsa yana ga wadanda aka yi mawa.
Tunda kayan gwamnati kayanmu ne na me zan taba su ko in bari a taba su? Matashi ya sani idan aka yi rikici, shi mai mulki ya saci kudinmu. Zai ta da hannunsa ne, ya kara gaba. Mu zai bari wadanda aka yi wa satar. Sai kuma abin daAllah Ya kwatar mana daga aikin da aka yi na kudinmu da aka ba su.
Da ina cikin matasa ba zan kai wa wadanda ba addininmu daya ko wadanda muke da bambancin kabila farmaki ba. Wai ma saboda me? Saboda siyasa? Ai wani rai ba ya daukar laifin wani ra!’ Kuma idan na kai hari ga wadansu aka kai wa ’yan uwana a wani wuri; me aka yi ke nan? Idan da ni matashi ne, duk wanda ya yi safarar kwaya in sha, in yi bangar siyasa, don hankalina ya fita in aikata abin da yake nema, ba zan sha ba. Amma kuma zan yi kamar na sha in koya masa hankali, in ce ai ina cikin maye ne.
Da ina daga cikin matasa zan yi amfani da hankalina ga duk abin da zan yi, zan tsara nuna fushina a tsanake, yadda zai yi tasiri, kuma ya yi amfani, ba tare da cewa na gwada ni ba ni da wayewa ba.
Wannan ’yar shawarar na yi ta ga ’yan kannenmu na Katsina, amma in matashin wata shiyya ya karanta ya ga abin amfani masha Allah, kowa na iya amfani da ita. Gaskiyar magana wannan shawara tawa mai tsada ce, don har na so in ce ban da Bagobiri da Banufe da Bahadeje. Duk da cewa wadannnan bayinmu ne, na amince matasansu su yi amfani da ita.
Danjuma Katsina, dan jarida ne, marubuci da ke zaune a Katsina.
08035904408
email:[email protected]