Matasa ba su so a sayar wa Atiku Abubakar fili a Yola
Al’ummar da ke zaune a Unguwar Wuro Chekke da ke Yola maso Kudu sun hana a sayar da fili ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.Mazauna unguwar sun ce bai kamata mai Unguwa Sa’ad Bawuro na Yola maso kudu da mataimakin mai unguwa Fadde Ibbi da Malam Ibrahim Kawu da Tijjani Mijinyawa da wani ma’aikacin […]
Al’ummar da ke zaune a Unguwar Wuro Chekke da ke Yola maso Kudu sun hana a sayar da fili ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Mazauna unguwar sun ce bai kamata mai Unguwa Sa’ad Bawuro na Yola maso kudu da mataimakin mai unguwa Fadde Ibbi da Malam Ibrahim Kawu da Tijjani Mijinyawa da wani ma’aikacin hukumar bada ruwa Modibbo Bappare su sayar da wannan filin ga tsohon mataimakin shugaban kasar ba domin filin na ’yan unguwa ne.
Manyan ’yan unguwar dai wadanda suka kunshi Alhaji Ahmed Bibi da Bala Babaiyali da Mohammed Bello Sa’idu da Kabiru Ali da Salihu Musa sun rubuta kaorafi sun kai wa Lamidon Adamawa da cewa ya yi amfani da ikon da Allah Ya ba shi domin kwatar musu hakkinsu domin hana sayar da wannan fili.
Sun kara da cewa “mu matasan Wuro Hausa muna so a yi mana bincike game da sayar da wannan filin da aka yi domin akwai wutar lantarki da kuma ruwan tuka-tuka wanda gwamnati ne ta yi domin mu samu cigaba a Faddi Ibbi a Wuro Hausa. Bai kamata a sayar da filin da muke amfana da shi ga Atiku Abubakar ba.”
“Muna so a taimaka mana a kwace wannan fili daga hannunsa domin in har aka bar masa, mu mutannen unguwar ba za mu amfana ba.”
Matasan dai sun nemi Lamidon da ya shiga wannan maganar domin kwatar musu hakkinsu domin kada a samu matsala.
Da aka tambayi Mai unguwa Alhaji Sa’ad Bawuro ya ce wannan abu ya yi matukar ba shi mamaki game da yadda matasan unguwar suka yi bore na babu gaira babu dalili.
Ya ce, wannan fili da matasan ke korafi a kai ba na gwamnati ba ne, filin wasu mutane biyar ne wadanda suka ga damar sayar da filinsu ga jami’ar Amurka da ke Yola (AUN) . “In har masu fili suna son sayar da filinsu yaya zan hana su sayarwa?” Inji shi.
“A gaskiya na yi matukar mamaki yadda na ga wadannan matasa suke daukar hotunan filayen gwamnati kuma suna cewa wai na sayar da filin gwamnati. Wannan zance dai karya ne domin wadannan filin da suke cewa an sayar karya suke yi.” Inji shi.
Ya kara da cewa,masu fili suna nan kuma don son kansu suka sayar da wadannan fili ga jami’an Amurka ta Yola kuma babu wanda ya tursasa su. Kuma tun da suna raye, za su iya yin shedar wadannan filayen da ake cewa ba nasu ba ne na gwamnati ne.