Matasa biyu sun yi amfani da suna dan majalisa sun damfari shugabannin kananan hukumomi a Kano

Wasu matasa sun gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Gyadi-gyadi da ke birnin Kano bisa zargin damfara ga shugabannin riko na wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kano, inda suka yi amfani da sunan wani dan majalisar dokokin jihar.Mai gabatar da kara a gaban kotun Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa wadanda […]

Matasa biyu sun yi amfani da suna dan majalisa sun damfari shugabannin kananan hukumomi a Kano
Matasa biyu sun yi amfani da suna dan majalisa sun damfari shugabannin kananan hukumomi a Kano

Wasu matasa sun gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Gyadi-gyadi da ke birnin Kano bisa zargin damfara ga shugabannin riko na wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kano, inda suka yi amfani da sunan wani dan majalisar dokokin jihar.
Mai gabatar da kara a gaban kotun Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargi, Abdullahi Tsaure (wanda ya gudu) da Umar Salihu mai kimanin shekara 25 haifaffen garin Malumfashi a Jihar Katsina sun yi sojan gona da sunan Alhaji Lawan Safiyanu Gogori, Shugaban Kwamitin Al’amuran kananan Hukumomi na Majalisar Jihar Kano ne wajen damfarar shugabannin.
Ya ci gaba da cewa a ranar 6/8/2013 da misalin karfe 3:00 na yamma dan majalisar ya kai kara ga ’yan sanda cewa kimanin wata uku da suka wuce wadanda ake zargin sun yi amfani da sunansa suka karbi Naira dubu 350 daga hannun shugabannin riko na kananan hukumomin Tofa da Kibiya da Rano da Tarauni.
Alhaji Gogori ya bayyana wa kotu cewa wadanda ake zargin sun yi yunkurin karbar wasu kudin daga hannun Shugaban riko na karamar Hukumar Nassarawa da ke jihar, amma ba su samu nasara ba.
A lokacin da ake saurara karar wanda ake zargi na farko Abdullahi Tsaure ya gudu yayin da Umar Salihu ya amsa laifuffukan da ake zarginsu na sojan gona da bata suna wadanda suka saba da sashi na 187 da 175 na dokar Penal Code ta shekarar 2000.
Alkalain Kotun Mai shari’ Habibudden Sulaiman Sharifai ya daga saurar karar zuwa ranar 21 ga Oktoba tare da ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan kaso.