Matasa da ’yan kasuwar Bwari sun koka game da kona kasuwarsu

’Yan kasuwar da suka yi asarar dukiya a sakamakon kona kasuwar Bwari da ake zargin wasu matasa da banka mata wuta, sun bayyana korafi a kan kin hukunta wadanda ake zargi da hannu a lamarin bayan an kama wasu daga cikinsu da farko. Jagoran ’yan kasuwar Alhaji Shehu Muhammed wanda ya bayyana hakan a yayin […]

Matasa da ’yan kasuwar Bwari sun koka game da kona kasuwarsu

’Yan kasuwar da suka yi asarar dukiya a sakamakon kona kasuwar Bwari da ake zargin wasu matasa da banka mata wuta, sun bayyana korafi a kan kin hukunta wadanda ake zargi da hannu a lamarin bayan an kama wasu daga cikinsu da farko.

Jagoran ’yan kasuwar Alhaji Shehu Muhammed wanda ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da ’yan jarida a ranar Laraba, ya ce rasa aiwatar da hukuncin na iya karfafa wa wasu gwiwa su aikata irin hakan a gaba. “Hukumomin ba da dauki irinsu NEMA da kuma takwararta na yankin Birnin Tarayya sun ba da gudunmowar kayan agaji ga ’yan kasuwar ta hannun karamar hukumar, sai dai a cewarsa an karkatar da kayan ga wasu da lamarin bai shafa ba, sannan ragowar aka bai wa wasu jami’an karamar hukumar ba tare da mu da lamarin ya shafa an ba mu komi ba,” inji shi.

’Yan kasuwar sun ce har zuwa ranar, Sanatan Abuja Philip Tanimu Aduda bai kai masu ziyarar jaje ba, haka nan dan Majalisar Tarayya na yankin, Zephaniah Jisalo da kuma Esu Bwari J.P Ibrahim Yaro, in ban da Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro da ya shigo wajen ya jajanta musu.

’Yan kasuwar sun ce ba za su amince da shirin mayar da su zuwa wani sabon waje ba kamar yadda shugaban karamar Hukumar Mista Musa Dikko ya bukace su da su yi, kasancewar wajen ginanniyar sabuwar kasuwa ce da ke bayan gari wadda ba su da ko shago guda a wajen kuma shaguna ne na wadanda ba ’yan kasuwa ba da aka riga aka gina tun a baya.

A nasu bangaren, kungiyar matasa na garin Bwari wadda ba ta Gbagy ba, ta bayyana korafi a kan wasu bayanan batanci da ke kara-kaina a yanar gizo da suka zargi wata kungiya da ke garin da yayatawa.

Bayanin wanda Malam Abubakar Abdullahi ya bayyana a madadin sauran mambobinta, ya ce yawancin bayanan da ake bayyanawa a matsayin dalilian da suka jawo rikicin, bayanai ne na karya. kungiyar ta bukaci Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello da ya tilasta wa karamar Hukumar Bwari biyan diyya ga ’yan kasuwa da suka yi asara da wadanda aka kona wa gida ko abun hawa, ta hanyar zabtare kudin karamar hukumar daga asusun Birnin Tarayya a kowane karshen wata. kungiyar ta bukaci Ministan da ya kafa kwamitin bincike a kan lamarin.

Matawallen Esu Bwari, Mista Joseph dantani Baba, wanda ya zanta da wakilinmu a madadin Esu Bwari J.P Ibrahiim Yaro, ya danganta daukacin rigimar da takaddama a kan sarauta na garin, da ya zargi wata gwamnatin a baya da haddasawa. Ya ce cikakken zaman lafiya a yankin zai samu ne idan hukuma ta yi adalci ta hanyar tabbatar wa kabilarsu da sarautar wajen ita kadai sannan ta kawo karshen na bangaren sarki wanda ya ce ba dan asalin yankin ne ba.