Matasa da yunkurin rike madafun iko a zaben 2019

Sha’anin mulki ko shugabanci ba abu ne na wasa ba, ba kuma abin da za a rika ganganci da rayuwar al’umma ba, saboda haka lallai yana da matukar muhimmanci a san su wa ya kamata ya shugabanci al’umma, babu zancan babba ko yaro ko tsoho ko matashi,  a dubi nagarta da cancanta. Misali rashin bai […]

Matasa da yunkurin rike madafun iko a zaben 2019
Matasa da yunkurin rike madafun iko a zaben 2019

Sha’anin mulki ko shugabanci ba abu ne na wasa ba, ba kuma abin da za a rika ganganci da rayuwar al’umma ba, saboda haka lallai yana da matukar muhimmanci a san su wa ya kamata ya shugabanci al’umma, babu zancan babba ko yaro ko tsoho ko matashi,  a dubi nagarta da cancanta.

Misali rashin bai wa matasa dama su samu guraben mukamai na nadi ko na zabe yana da muhimmanci? Kuma har in sun shigo gwamnati za su samu damar da ta kamata in an yi la’akari da yadda manya suka ji zakin mulki? Yaya shugabannin baya suka tafiyar da kasar nan lokacin da kowa ya san suna matasa wajen dattaku, amana, kishin kasa, haka matasan yanzu suke?

Matasan wannan lokaci za a iya cewa sun bar baya da kura, domin duk wanda suka mara wa baya to dayan biyu ne, ko dai don ya ba su kudi ko ya yi musu alkawarin mukamai in ya ci zabe. Ka ga a nan ina kishin kasa ga matasan wannan lokaci?

Sannan wani abu da ya sa mutanen wannan lokaci suka sakankance ya sa ba a jin amonsu ko saurarensu yadda ya kamata, sai dai a yi amfani da su a ci zabe, saboda toshewar basira. Lallai matasan yanzu suna da jan aiki ta cimma burinsu ta fuskar shugabancin kasa.

Wai shin ina tunanin matasan wannan lokaci da ake amfani da su a ba su makami da kwayoyi domin su cuci al’umma su cutar da kawunansu da kasa baki daya, saboda dan abin da za a ba su da ba zai share musu hawaye ba?   A nan sai su tambayi kawunansu cewa  ina ’ya’yan wadanda suke sa su? Ka ga ko dai suna kasashen waje suna karatu ko an boye su a gida suna cin kaji ko farfesu, an bar ’ya’yan talakawa cikin duhun jahilci da talauci da cin dunduniyar junansu. ’Ya’yan masu fada-a-ji su yi ilimi mai kyau kuma su zo su ci gaba da shugabantarsu suna gallaza musu.

Yanzu duk irin wadannan matasa ba zai sa su sake tunani su koyi darasi kamar yadda matasan da, irin su Malam Aminu Kano da sauransu suka yi ba? Batun rike madafun iko, yana da kyau mu gaya wa kawunanmu gaskiya, shugabanci a hannun matasan wannan lokaci ba zai yiwu ba, akwai sauran lokaci har sai sun kara sanin ciwon kansu.

Su kansu wadanda suke da dan dama-dama a matasan ma’ana wadanda suka yi ilimi, ko dai a yi amfani da su wajen rusa kasa ko kuma su zama ’yan amshin Shata ko karnukan farautar masu rike da madafun iko, ko kuma in an yi sa’a sun samu mukamai, sai ka same su da yin almubazzaranci ko kece-raini da gina kawunansu kawai, amma ba wai su gina kasar ba.

Hakika akwai matasa mutanen kirki masu kwazo da sanin ya kamata, wadanda idan aka ba su dama za su tabuka abin kirki, amma abin tambaya shin za a ba su damar da ta kamata su rike madafun iko?

Yanzu in ka tsaya ka dubi shekarun matasa tun daga shekara 15 zuwa 60, ka karanci adadin wadanda suke rike da madafun iko na siyasa ko na nadi a kasar nan, sai ka ga suna da yawa amma abin tambaya wane irin ci gaba suka kawo ga mahaifarsu ko karamar hukumarsu ko jihohinsu ballantana kasa baki daya?

Amma in aka ce za a yi maganar hayaniya da tashe- tashen hankula da take wa shugabanni baya ko da za a mutu sai ka same su a wajen, amma batun kishin kasa da ci gabanta babu abin da ya dame su.

Yanzu matasa nawa ne suka ajiye mukamansu da suke fantamawa a kan rashin gaskiyar da ake tafkawa? Matasa nawa aka raba da rayukansu a kan wata gwagwarmaya domin tabbbatar da ’yanci da adalci a kasar nan daga shekara 20 zuwa yanzu? Ko matasa nawa aka kulle a gidan yari sakamakon wata gwagwarmaya ta tabbatar da ci gaban kasar nan? Gaskiya babu ko daya.

A zamanin da duk wanda ya zama wata tsiya sai ka tarar an daure shi a kurkuku, ba sau daya ba, ba sau biyu ba saboda nema wa talakawa ’yanci. Kai akwai wadanda suka rasa rayukansu a wancan lokaci, amma matasan yanzu za su iya zama yini guda a kurkuku saboda wata gwagwarmaya? Matasan yanzu kyale su da son kwalliya da kece-raini kullum a wanke goma a tsoma biyar da sharar barci da kwalisa, nan suka fi kokari.

Za ka ji matasa ana hira da su a kafafen watsa labarai ko yin wasu kungiyoyin matasa in suna bayani sai ka ga a baki ne kawai, amma da zarar sun samu dama ta wata kujera, in ana ba da maki sai an yi da gaske za ka ba su maki 20 a cikin 100.

Sannan matasan wannan zamani suna da wasu dabi’u na son yin dukiya a dare daya, suna son jin dadi ba tare da sun sha wahala ba, da son harkokin kashe kudade da dogon buri ko takama da asali, ga bushasha da jiji da kai, duk ko zuciyar da ta hada wadannan abubuwa, ba za ta taba nuna gaskiya da adalci a wajen shugabanci ba. Kuma iyayen wannan zamani sun cusa son abin duniya a zukatan ’ya’ya da kuma son ’ya’yan, ba ruwansu da me kake yi wajen samun kudi, su dai a yi ta kawo musu.  A nan kai ne da nagari tamkar da goma babu zancen a ina kake samo wannan dukiya?

Wani misali shi ne da yawa a kasashen duniya suna bai wa matasa damar rike mukamin kansila inda suka fi kusa da jama’a to sai a auna wane irin ci gaba suka kawo a kasar nan wajen hada kan jama’a da taimaka wa juna? Amma sai ka ga daga wanda ya yi aure sai wanda ya sayi gida ya bar unguwar da aka zabe shi ya sayi mota yana kece-raini, wanda mukamin kansila kamata ya yi a bai wa gogaggen ma’aikaci da ya yi ritaya kuma shekaru suka yi masa nisa, saboda yana cikin jama’arsa da zama, domin zai iya zama da jama’a a tattauna a samar da mafita.

Sannan wata annoba wacce take damun matasan wannan lokaci ita ce hudubar abokai ko kawaye, ko da yaro yana da dabi’u masu kyau sai ka ga abokai sun sa shi a harkar banza.

Haka su kuma mata da suke kururuwar lallai a ba su gurabe na mukamai, su ma suna da wasu matsaloli masu yawa da suka kamata su lura da su a kan kansu, domin shugabancin jama’a ba ya son rauni da bushasha da jan aji da kece-raini wajen biki ko almubazzaranci da dukiya. Saboda haka su ma mata suna bukatar shawarwari. masu kyau kafin su fara sha’awar rike madafun iko domin jagorantar jama’a.

 

Abdullahi Idris Yakasai

G.s.m 08054407095

Email: [email protected]