Matasa: kashin Bayan al’umma

Daga Nabeela Khalil Matasa na da wani kebantaccen matsayi na musamman a cikin kowace al’umma; sune kashin bayan kowace al’umma kuma sune jagorar cigaba da kawo canji cikin al’umma; duk wata tafiyar da ba matasa a ciki to gurguwar tafiya ce.In muka duba baya cikin tarihi, zamu ga cewa matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen […]

Matasa: kashin Bayan al’umma
Matasa: kashin Bayan al’umma

Daga Nabeela Khalil

Matasa na da wani kebantaccen matsayi na musamman a cikin kowace al’umma; sune kashin bayan kowace al’umma kuma sune jagorar cigaba da kawo canji cikin al’umma; duk wata tafiyar da ba matasa a ciki to gurguwar tafiya ce.
In muka duba baya cikin tarihi, zamu ga cewa matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen kafuwa da yaduwar kyakykyawan addininmu na musulunci madaukaki; jibi irin dauriya, jajircewa, sadaukarwa da suka nuna a lokutta daban-daban.
Babanmu Annabi Ibrahim AS ya na Matashi ya ja da al’ummarsa gabadayanta game da bautar gumaka da suke yi wanda har ta kai ga sun banka wuta sun kona shi. Mu duba ga hakuri da juriyar Annabi Isma’il, yana dan matashi, amma ya bai wa mahaifinsa kwarin gwiywar aiwatar da hukuncin Allah akansa na yankashi kamar yadda Babansa AS ya gani a mafarki. Jibi dauriyar Annabi Yusuf AS lokacin da aka jefa shi cikin rijiya da kuma iri-irin jarabawar da ya fuskanta na zaman kurkutu da sauransu. Jibi irin gwagwarmayar da Annabi Musa Ya sha yana Matshi da Fir’auna da kuma mutanensa Baniy Isra’ila. Sannan shi kan shi Annabinmu SAW Ya kasance yana matashi aka saukar mashi da Annabci; misalan matasa abin koyi a cikin gwagwarmayar addini sun hada da:
Sayyidina Aliy RA wanda shine matashi na farko da ya amshi musulunci; bayan haka abubuwan jarumtaka da sadaukarwar da yayi wajen kafuwar addinin musulunci ba su da iyaka.
Mu’az bin Jabal ya kasance shine jakadan musulunci na farko; kuma ya kasance ba wanda ya kai shi sanin ilmin halal da haram a cikin al’umma; shine sarkin malamai ranar gobe kiyama; kuma duk ya tattara wadann abubuwa a cikin kankanen lokaci domin ya rasu yana da shekaru 32 kacal a duniya.
Ummuna A’isha ita ce mace ta farko da ta haddace kur’ani Mai Tsarki; ta zama babbar malama tana shekara sha takwas kadai har ya kasance Manyan Malamai daga nesa suna zuwa daukar darussa a wajenta.
Zaid bin Thabit yana da shekaru 13 kadai amma cikin zakuwa yake rokon Annabi SAW da yayi mashi izini ya rufa mashi baya zuwa yakin Badr, amma Annabi SAW bai yi mashi izinin ba saboda shekarunsa sun yi karanta sai dai yace da shi: ‘je ka koyo min rubutun  yahudawa’ abinda Zaid ya amsa cikin zafin nama.
‘Yan Aljanna Matasa ne!
Tirmidhi a cikin littafin Kitabin Siffatil kiyama wal raka’ik ya ruwaito cewa wata tsohuwa tazo tace da Annabi SAW Ya Manzon Allah yi mani addu’a in shiga Aljanna, sai yace da ita Ya Umm Fulana ai tsaffi basu shiga aljanna! Sai ta tafi tana kuka sai Annabi SAW yasa aka kirata sannan yace da ita ba zata shiga aljanna da tsufa ba, watau za a mayar da ita matshiya.

Ka ci ribar kuruciyarka…
Manzon Allah SAW yace ‘ka ci ribar dinka kafin wata biyar din; sune:
•    kuruciyarka kafin tsufanka;
•    Lafiyarka kafin rashin lafiyarka;
•    Arzikinka kafin talaucinka;
•    Lokacinka kafin ya zama baka da lokaci
•    Rayuwarka kafin mutuwarka.
Yana daga cikin matsalar matasa a wannan lokaci na mu shagalta da rayuwar duniya da jingine yin abubuwa masu muhimmanci zuwa ga yin wadanda ba su da mahimmanci. Na san da yawanmu nan muna kin aiwatar da muhimman abubuwa,  musamman wadanda suka shafi addininmu, mu runka cewa ai nan gaba ma yi, mu sani, duk wani abu da mutum ya kasa aiwatarwa lokacin kuruciyarsa da wuya ya iya yin abin nan ko bayan ya tsufa. Don haka lokacin kuruciya, lokacin da mutum ya ke da yawaitar kuzari shi ne lokacin aiwatar da duk wani muhimmin abu, musamman wanda ya danganci addini da abin da zai tserar da shi daga wuta ranar gobe kiyama.; maimakon matashi ya kashe dare yana kallon kwallo ko fina-finan nasara gara yayi sallar tsayuwar dare koda ta tsawon minti talatin ne kawai.
1.    Tambayar Dole ce Ranar Gobe:
Manzon Allah SAW ya ce Bawa ba zai matsa daga gaban Ubangijinsa SWT ba har sai ya tambayesa game da abubuwa guda 4:
•    Rayuwarsa: Me ya yi da ita?
•    kuruciyarsa: Akan mi ya raye ta?
•    Dukiyarsa: Ta wace hanya ya tara ta?
•    Ilminsa: Ya ya yi da shi?
Tambayar farko ta kasance akan rayuwa gabadayanta, daga ciki kuma sai aka kebance lokacin kuruciya saboda muhimmancinsa a cikin rayuwar dan’adam aka sake yin tambaya akansu. Haka kuma sauran tambayoyi biyun da suka biyo baya duk sun shafi lokacin kuruciya domin duk a lokacin ne ake nemansa, duk wanda bai yi su ba, har kuruciyarsa ta shige to da wuya ya yi su kuma.
2.    Daga cikin Karramammun Ranar Gobe:
Manzon Allah SAW yace akwai wasu mutane bakwai da za a karrama ranae gobe kiyama a shigar da su cikin inuwar al’arshi Ubangiji SWT, ranar da ba wata inuwa sai Ita. Daga cikinsu akwai matashi da ya  kare kuruciyarsa akan hanyar bautar Allah da taimakon addininsa. Saboda muhimmancin wannan lokaci, da kasancewarsa mai cike da hadurra da jarabawowi; lokacin da zuciyar kowane matashi ke cike da sha’awowin rayuwa iri-iri, duk wanda ya daure ya cije, bai biye ma son zuciyarsa ba, lallai Allah zai saka masa da mafi kyawon sakamako; daya daga ciki shine wannan karramawar da muka fada a baya. Don haka matasa sai a dage da yawan zuwa masallaci, sauraren wa’azzu da nasihohin malamai da yin aiki da su; kyautatawa ga iyaye; dagewa wajen neman ilimi da wajen neman na kai; kannewa wajen kokarin bin Allah komin tsananin yanayin rayuwa da taimakon addini da al’umma a koda yaushe. Da haka sai matsahi ya ga ya tashi ya zama abin alfaharin al’ummarsa, kuma sanyin idon iyayensa. Amma in matashi ya biye ba sha’awowi da kuma zugar shaidan, to karshensa ba zai yi kyau ba, kuma sai ya je lahira Allah SWT Ya hukunta shi akan sabon da ya yi. Da fatan Allah Ya taimakemu da bin dokokinSa a kowane yanayi muka sami kanmu, amin.

Nabeela Khaleel ta rubuto ne daga Jihar Katsina

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50