Matasa ku yi amfani da kafafen sada zumunta wajen zaben shugabanni nagari – Dokta Nazifi

Wani malami a sashen Bunakasa Tattalin Arzikin kasa a Jami’ar Abuja, Dokta Nazifi Abdullahi Darma ya shawarci matasan kasar nan da su wayar da kan junansu kan zaben nagartatun shugabannin domin samun tabbtacciyar makoma. Dokta Nazifi ya yi wanann kira ne yayin gabatar da makala a wajen taron lakca na shekara-shekara da Cibiyar kwararau akan […]

Matasa ku yi amfani da kafafen sada zumunta wajen zaben shugabanni nagari – Dokta Nazifi

Wani malami a sashen Bunakasa Tattalin Arzikin kasa a Jami’ar Abuja, Dokta Nazifi Abdullahi Darma ya shawarci matasan kasar nan da su wayar da kan junansu kan zaben nagartatun shugabannin domin samun tabbtacciyar makoma.

Dokta Nazifi ya yi wanann kira ne yayin gabatar da makala a wajen taron lakca na shekara-shekara da Cibiyar kwararau akan Harkar Safiyo ta kasa reshen Jihar Kano ta shirya, mai taken Ci gaban tattalin arziki da kuma kalubalensa: gudummawar kwararru wajen sake bunkasarsa. Dokta Naizifi ya bayyana cewa a maimakon yin amfani da kafafen sada zumunta na intanet da matasan ke yi wajen surutan banza kamata ya yi su yi amfani da wadannan kafafe wajen wayar da kan juna akan yadda za su fito da nagartatatun shugabanni wanda za su sama musu makoma mai inganci. 

“Ga shi yanzu muna da kafafen sada zumunta na intanet a maimakon amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, akwai bukatar matasanmu su fito su ganar da juna bukatar dake gabansu wajen zaben

shugabanni na kirki. Duk wani gyaran tattalin arzikin kasa da ake son a yi idan ba a gyara shugabanci ba za a sami nasararsa ba, Haka kuma idan an gyara shugabancin ba a samu an gyara yadda ake yin dokoki ba to ba za a ci nasara ba.”

Dokta Nazifi ya kara da cewa canji ba zai faru katsahan ba har sai mutane sun yi hobbasa wajen samar da shi “A duk inda aka sami canji a kasashen duniya idan ka bincika za ka ga cewa mutane ne suka yi wani hobbasa wajen samuwarsa. Idan ka duba lokacin da Donald Trump ya ci zabe ya yi tunanin zai iya yin wani abu a kansa inda har ya lashi takobin cewa akwai kasashen da ba za su shigo Amurka ba, amma saboda hukumomin kasar masu karfi ne sai ga shi bayan ya hau mulki karamar kotu ta hana shi gudanar da wannan aniya tasa.