Matasa masu kwace kayan mutane sun shiga hannu a Legas
Rundunar ’yan sanda a Legas ta yi nasarar kame wasu gaggan ’yan awawa da suka addabi jama’ar Agege da kewayenta.Tuni dai waɗannan tsagerun suka yi ƙauri suna a yankin, inda suke tare mutane suna ƙwatar kayayyakinsu, waɗanda suka hada da kuɗaɗe, wayoyin salula, sarƙar gwal da dai sauransu. Sun yi ƙaurin suna matuƙa ta yadda […]
Rundunar ’yan sanda a Legas ta yi nasarar kame wasu gaggan ’yan awawa da suka addabi jama’ar Agege da kewayenta.
Tuni dai waɗannan tsagerun suka yi ƙauri suna a yankin, inda suke tare mutane suna ƙwatar kayayyakinsu, waɗanda suka hada da kuɗaɗe, wayoyin salula, sarƙar gwal da dai sauransu. Sun yi ƙaurin suna matuƙa ta yadda suka addabi jama’a a yankin.
Da yake gabatar da su a ƙarshen makon jiya, shugaban rundunar ta Task Force a Legas, SP Olayinka Egbeyemi ya shaida wa manema labarai cewa rundunar ta yi nasarar kame madugun ’yan awawar mai suna Tobi Akinbayo, wanda ake wa laƙabi da ‘dan Kunama’ da Muyideen Olayinka da kuma Ibrahim Olaniran a unguwar Dopemu, Agege a Legas.
Ya ce ana tuhumar su ne da muggan laifuka waɗanda suka haɗa da fashi da fyaɗe da ma ɗaukar rayukan jama’a, domin sukan yi yunƙurin kisan duk wanda ya yi ƙoƙarin kawo masu cikas a mugunyar sana’ar tasu.
Ya shaida cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, domin kawar da miyagun ayyuka na tsagerun. Ya kuma yi kira ga jama’a da su dinga yin kaffa-kaffa kuma su rika ba da rohoton duk wani ɓata-gari da ba su yarda da shi ba.
Madugun ’yan awawan, Tobi Akin bayo ɗan shekaru 28, wanda ɗan asalin Abekuta ne da ke zaune a unguwar Salako a Dopemu, Legas ya amsa laifin da ake tuhumar su da shi na fashi da ƙwace da yin fyaɗe dama kisan jama’a. Ya ce suna aikata masha’ar ne a sassa daban-daban na Legas, a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar da yake jagoranta.