Matasa mu kama sana’a
Hakika ba karamin tashin hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takaimaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin hakan ne ke sa dimbin matasa aukawa cikin miyagun ayyuka irin su; sace-sace da shaye-shaye da bangar siyasa da sauransu. A wani bangaren ma sana’a ta fi muhimmanci fiye […]
Hakika ba karamin tashin hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takaimaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin hakan ne ke sa dimbin matasa aukawa cikin miyagun ayyuka irin su; sace-sace da shaye-shaye da bangar siyasa da sauransu. A wani bangaren ma sana’a ta fi muhimmanci fiye da wani ilimin, dalili shi ne sau tari matasa da yawa masu ilimi sukan yi amfani da iliminsu ta hanyoyin da ba su dace ba, sakamakon rashin sana’a inda wani lokacin ma ba za ka iya bambance matashi mai ilimi da marar ilimi ba, kamar wajen shaye-shaye da sace-sace inda dukkansu sukan shiga riga iri daya.
Saboda haka nake kira ga ’yan uwana matasa, masu karatu da marasa karatu, cewa mu fantsama ga harkokin kasuwanci domin neman halal dinmu da taimakon kanmu da iyayenmu, maimakon ci gaba da zaman muna jira daga wajen gwamnati ko yayye da iyaye. Lokaci ya yi da za mu farka daga dogon barcin da muke.
Ta yaya za mu fara kasuwanci? Wannan tambaya ce mai ma’ana ganin cewa akwai sana’o’i da yawa wadanda gurbatattu ne. To amma a nan muna magana ce a kan sana’o’i na halal musamman wadanda muka gada daga wajen iyaye da kakanni. Misali akwai, noma da kira da saka da fatauci da sauransu. Akwai kuma na zamani wadanda yanzu su ma za mu kira su da sana’a domin ta nan mutane da yawa suke cin abinci, kamar kasuwancin Intanet da kayan shago da daukar hoto da wankin mota da ginin zamani da kabu-kabu da sauransu.
Kadan daga cikin sana’o’in da na lissafo, wasu suna bukatar jari don farawa, wasu da yawa a cikinsu kuma kawai biyayya da neman izini suke bukata daga wajen iyayen gida masu yin irin wannan sana’a don farawa a matsayin yaro kafin kai ma ka koya a kai ga lokacin da kai ma za ka bude naka wajen sana’ar ko kasuwancin tare da janyo wadansu yaran don koya musu. Amma fa duk hakan zai faru ne in an yi hakuri. Allah Ya sa mu dace, amin summa amin.
Hussaini Abba Dambam, Karamar Hukumar Dambam Jihar Bauchi, (08020814173, 08140501505)