Matasa na farautar ’yan Boko Haram a Maiduguri
Matasa a bangarori da dama na garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno sun himmatu wajen farautar mutanen da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.Wata majiya ta sheda wa Aminiya cewa, matasan wadanda su ne suka sanya kansu wannan aikin domin taimaka wa jami’an tsaro, sun kama wadansu da suke zargin ‘yan Boko Haram ne a karshen […]

Matasa a bangarori da dama na garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno sun himmatu wajen farautar mutanen da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.
Wata majiya ta sheda wa Aminiya cewa, matasan wadanda su ne suka sanya kansu wannan aikin domin taimaka wa jami’an tsaro, sun kama wadansu da suke zargin ‘yan Boko Haram ne a karshen mako suka mika su ga rundunar tsaro ta hadin gwiwa (JTF).
Fiye da matasa 500 ne wadanda suka fito daga yankunan Gwange I da Gwange II da Blabrin da Mafoni da Hausari da ke cikin Maiduguri ne suka hada kai domin tunkarar ‘yan tsageran da ke lababowa suna komawa cikin garin Maidugurin, inda suke kama su suna mika wa hukuma.
Sai dai kuma da Aminiya ta tuntubi kakakin tsaro Birgediya Janar Chris Olukolade ya ce ba zai iya tabbatar da labarin ba, amma duk da haka sojoji suna maraba da duk wani goyon baya da za su samu daga jama’a.
Ana tunanin ‘yan kungiyar Boko Haram da dama ne suka sudado suka shiga cikin garin Maiduguri a sakamakon farmakin da sojoji suke kai musu bayan da Shugaba Jonathan ya ayyana dokar ta-baci kuma aka tura dakarun soja yankin arewacin jihar domin su tarwatsa masu tayar da kayar bayan kuma su kwato yankunan da ke karkashinsu.
“Mu matasan garin Maiduguri mun yanke shawarar zakulo duk wani dan Boko Haram da ya dawo cikin garin nan bayan sun fice zuwa kauyuka da dazuzzukan da sojoji suka tarwatsa su kwanan nan.’’ Inji shugaban ‘yan sintirin na yankin Gwange II.
Shugaban wanda ba ya so a bayyana sunansa ya ci gaba da cewa, “mu al’ummar Gwange II mun gode wa Allah domin zuwa yanzu mun kama fiye da ‘yan Boko Haram guda goma mun mika su ga sojoji, kuma mun ji dadi da muka ji su ma ‘yan uwanmu na Gwage I sun hada kansu domin gudanar da wannan aikin taimakon al’umma. Insha Allah ba da dadewa ba za mu shigar da wannan yunkurin cikin yankin GwangeIII da Gwange Ib har ma sauran al’umma su ma su bi sahu.
Wani ganau ya sheda wa Aminiya cewa wadansu matasa a yankin Hausari sun tsallaka zuwa cikin yankin Blabirin suka kama wadansu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da suka dawo suka mika su ga sojoji. “wannan abu da matasan Hausari suka yi ya harzuka wadansu ‘yan Boko Haram din wadanda suka yi kokarin shiga garin garin Maiduguri domin daukar fansa ta hanyar yin shiga kamar su kauyawa ne dauke da gawa za su je makabarta a cikin mota a-kori-kura, amma jami’an rundunar JTF suka cafke su. Inji wani mazaunin yankin.
Wata kafar yada labarai ta Afirka ta Kudu mai suna timeslibe.co ta tabbatar da faruwar wannan al’amarin inda ta ambaci mutanen yankin suna cewa,mahara guda 10 ne suka shiga yankin Hausari a cikin mota a-kori-kura dauke da makara a bayan motar. ‘’Kowa ya dauka za su je makarbarta ne, sai da suka fito daga motar suka fito da bindigogi suka rika yin harbi ko ta ina,’’ kamar yadda wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Aji ya bayyana.
Haka kuma kafar yada labaran ta ruwaito kakakin rundunar JTF Sagir Musa yana tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun kai farmaki ranar jumu’a da yamma a yankunan Hausari da Fizzan da Gwange.
Da wakilinmu ya zagaya cikin garin Maiduguri ya fahimci cewa mutanen garin suna farin ciki da wannan yunkuri na matasan, inda har yara kanana ke kwaikwayon matasan suna rera wakar da suke yi suna cewa, “komi ya yi farko zai yi karshe,’’ manyan mutane kuma suna yin musabaha da matasan suna cewa, “kun yi daidai, AllahYa kiyaye ku.’’
Matasan wadanda yawansu ke karuwa a kullum, sojoji ne ke yi musu laccar da za ta zama musu jagora a yayin gudanar da aikin sa-kan da suke yi, inji wani mazaunin garin.
Wadansu mazauna garin kuma suna taimaka wa matasan da ruwan leda, kuma zuwa lokacin rubuta wannan labarin matasan sun kama ‘yan Boko Haram guda 55 a yankunan Gwange I da Gwange II da Blabirin da Hausari, duk a cikin Maiduguri.
“Hakimai sun kira shugabanninmu suka bukaci mu ci gaba da kyakyawan aikin da muke yi kuma suka roke mu da mu kula kada mu kama wanda babu ruwansa. Inda muka tabbatar musu da cewa ba za mu kama duk wanda babu ruwansa mu ce shi dan Boko Haram ne ba.’’ Inji wani jagoran wata kungiyar sintirin.
Jagoran wanda ba ya so a bayyana sunansa ya ci gaba da cewa, “mu a bangarenmu na Gwange II duk wanda zai shiga cikin wannan aikin da muke yi sai mun ba shi Alkur’ani ya rantse cewa ko da wasa ba zai fadi sunan wanda babu ruwansa ba ya ce shi dan Boko Haram ne ba. Kuma kowa daga cikinmu sai ya fadi sunan duk wani mutum ya taba da bindiga, ko dan uwansa ne kuwa, daga nan sai mu dunguma gaba daya mu je mu kama wanda aka ce dan Boko Haram ne, sannan duk wani matashin da yake bukatar shiga cikinmu sai ya cika wadansu ka’idoji tukun.’’
Wani jagoran kuma da ba ya so a bayyana sunansa da wakilinmu ya tambaye shi yadda suke gane dan Boko Haram sai ya ce, ‘’Ai wadannan ‘yan tsageran suna tare da mu ne a da, daga baya ne suka ware kansu daga cikin al’umma suka yi sansaninsu a wajen gari, domin haka ba za mu samu wata matsala ba wajen gane su. A yanzu haka muna aiki tare da sauran ‘yan uwanmu da ke sauran unguwanni domin sanin duk samun sunan duk wanda ya shiga cikin kungiyar Boko Haram, muna da littafin da ke dauke da sunayen ‘yan Boko Haram din da muke nema, zuwa yanzu mun kama wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne su 55 daga cikin unguwanni daban-daban na garin Maiduguri.’’ Inji shi.
A halin yanzu dai a sakamakon rufe hanyoyin shiga arewaci da kuma kudancin jihar Borno, mazauna yankunan karkara suna cikin mayuwacin hali saboda karancin abinci, domin ba za su iya zuwa kasuwanni su sayi abincin ba.
Da yake bayani game da al’amarin,kakakin rundunar soja Olukolade ya ce dakarun musamman da aka tura suna binciken ababen hawa ne kawai a wadansu hanyoyi da aka ware, kuma ko shakka banu binciken da ake yi yana haifar da jinkiri ga matafiya, amma ya roki matafiyan da ke bin wadannan hanyoyin da su kara hakuri da sojojin da ke aiki a kan hanyoyin.