Matasa ne kashin bayan zaman lafiya – Shugaban Al’umma

Shugaban kwamitin tsaro, hadin kai da kuma zaman lafiya a Kurosriba, Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin kwamitinsa cewa zai zage damtse domin ganin matasan jihar, musamman ’ya’yan ’yan Arewa mazauna Kurmi ba su shiga harkoki da za su rika zubar da mutuncinsu da na iyayensu ba a duk fadin jihar, domin kuwa […]

Matasa ne kashin bayan zaman lafiya – Shugaban Al’umma

Shugaban kwamitin tsaro, hadin kai da kuma zaman lafiya a Kurosriba, Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin kwamitinsa cewa zai zage damtse domin ganin matasan jihar, musamman ’ya’yan ’yan Arewa mazauna Kurmi ba su shiga harkoki da za su rika zubar da mutuncinsu da na iyayensu ba a duk fadin jihar, domin kuwa su ne kashin bayan zaman lafiya a kasa.

Shugaban ya furta haka ne a jawabin marhabun lale da ya yi lokacin da wakilan Kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar, karkashin jagorancin Babban Darakta a ma’aikatar, Mista Emmanuel B. Ekpenyong da mataimakiyarsa Uwargida Immaculata E. Ekpenyong suka kawo wa kwamitin ziyarar gani da ido a ofishinsa da ke Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa da ke Kalaba. 

Ya ci gaba da cewa: “Mun kafa wannan kwamiti ne domin tarbiyantar da ’ya’yanmu da nufin hana su shiga nau’o’in tsageranci, kungiyanci da makamantan duk wani aiki da zai haddasa husuma, domin kuma mu hada hannu da gwamnatin jiha da ta tarayya wajen bayar da gudunmawa wajen tsaro saboda larura ce ba ta gwamnatin jiha ko tarayya ba; a’a sai domin magance kalubalen tabarbarewar tsaro da galibi ya zama ruwan dare a duniya.”

Ya kuma bayyana gamsuwarsa matuka yadda ya lura matasa da suke zuwa daga jihohin Arewa cin rani suka rungumi sana’a, suna neman arziki; ba su shiga harkokin kungiyoyi da kuma harkokin shaye-shaye. “Za mu ci gaba da daukar mataki na ganin mun dakile duk wata harka ta shaye-shaye da masu zuwa suna bata mana unguwa,” inji shi.

Daga nan ya gargadi matasa da su guji sayen kayan sata da kuma saye da sayar da kayan maye, domin duk wani wanda aka kama zai dandana kudarsa. Ya ce idan aka samu mutum da laifi babu ruwan kwamaitinsa da shi.

Da yake mayar da jawabi, jagoran tawagar, Mista Emmanuel, a madadin kwamishinan ya ce: “A gaskiya mun gamsu da yadda muka zo muka ga ashe har da shugabann addini da sarakuna ke jagorantar wannan kwamiti.

“Mun ji dadin yadda kuka shigo domin taya mu bayar da gudunmawa wajen harkar tsaro. Ai mu da ma Jihar Kurosriba jiha ce ta zaman lafiya ba kuma za mu taba bari wani ya zo daga wata jiha ko yanki ba ya cusa mana wata akida ta daban ba. Ku ma Hausawa kuna da tarihin zama Kurosriba mai kyau, domin ba a taba samunku ko hannunku a wani yamutsi ba,” inji shi. 

Shi kuwa Alhaji Sani Baba Gombe da ke karamar Hukumar birnin Kalaba ya tambayi kwamishinar cewa su da aka haife su a jihar, su ma suka haifa, me ya sa ba a ba su katin shaidar zama dan kasa kuma ba a daukar su aikin gwamnati a matakin jiha? Shi ne uwargida Immaculate ta amsa da cewa: “Magana ta gaskiya mu a nan Kurosriba ba za mu iya daukar muku alkawari ba na daukar aiki. A mataki na gwamnatin jiha, na san ana tafiya da ’yan Arewa a gwamantin jiha, ana nada maku shugaban Hukumar Alhazai da kuma ba ku damar nada sarakunanku kana kuma a wannan gwamnati an nada muku mai ba gwamna shawara kan al’amuran baki. Shawarar da zan ba ku a nan ita ce, ku rika nema masu a Gwamnatin Tarayya. Idan an kawo wani babban ma’aikaci daga Tarayya, ku rika mika mksu bukatunku, za su taimaka.

“Game da batun katin shaidar zama dan asalin jihar kuwa, a gaskiya wannan matsala ruwan dare ce a Najeriya. Akwai dan uwana mazaunin Kano ne, can ma ya hayayyafa. Idan wani abu ya taso na karatun ’ya’yansa shi ma gida yake dawowa yana yi masu. Ba zan yi karya ba domin a so ni,” inji ta.