Matasa ne kusan rabin masu coronavirus a Najeriya

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta bayana damuwa cewa kashi 46 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutaro coronavirus a Najeriya matasa ne ‘yan shekara 21 zuwa 40. Minista a Ma’aikatar Lafiya, Olorunnibe Mamora ya sanar da haka a yaykiltar Minista Osagie Ehanire a taron jawabin kwamitin yaki da cutar na kasa karo na 57 […]

Matasa ne kusan rabin masu coronavirus a Najeriya

Yadda za a iya samun cutar Coronavirus ta amfani da wayar salula

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta bayana damuwa cewa kashi 46 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutaro coronavirus a Najeriya matasa ne ‘yan shekara 21 zuwa 40.

Minista a Ma’aikatar Lafiya, Olorunnibe Mamora ya sanar da haka a yaykiltar Minista Osagie Ehanire a taron jawabin kwamitin yaki da cutar na kasa karo na 57 ranar Alhamis a Abuja.

Ya yi kira ga matasa da su kula tare da yin abun da ya dace wajen kiyaye matakan kariyar cutar a kowane lokaci.

Mamora ya kuma bayyana damuwa kan yadda cutar wadda “abin takaici, ta yi ajalin mutum 956 a Najeriya’ ta yadu a tsakanin matasa.

Ya ce zuwa ranar mutum 33,943 sun warke daga cikin mutum 47,743 da suka kamu, ya bayyana cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen ganin an yi wa ‘yan Najeriya gwajin cutar domin su san matsayinsu.

Kawo yanzu mutum 338,084 ne aka yi wa gwajin cutar amma manufar gwamnati shi ne ganin an yi wa mutum miliyan 20 gwajin cutar a Najeriya, kamar yadda ya ce.

A cewarsa fiye da kashi 70 na gwajin da aka gudanar an yi ne a jihohi tara na Legas, Kano, Abuja, Filato, Oyo, Kaduna, Edo Ogun da kuma Ribas.

Kashi daya bisa hudun gwajin coronavirus kuma an yi ne a Jihar Legas ita kadai, inda cutar ta fara bulla ta kuma fi kamari da farko.

“Za mu ci gaba da aiki tare da gwamnatocin jihohi domin kara kaimi wajen gano masu cutar da kuma yin gwaji”, inji shi.

— Damuwa kan kamuwar jami’an lafiya da coronavirus

Ministan ya kuma damuwa kan yadda ma’aikatan lafiya ke kamuwa da cutar.

“Domin tabbatar da nasarar da muka samu wajen rage yawan jami’an lafiya masu kamuwa da cutar, mun horas da su a kan kariya da kuma kula da cututtuka masu yaduwa.

“A Jihar Abia mun horas da ma’aikatan lafiya 594 daga asibitocin gwamnati da masu zaman kansu kan yaki da cututtuka masu yaduwa.

“Yanzu muna bincike a kan cututtuka masu alaka da cibiyoyin kula da lafiya a Jihar Kaduna kuma abun da muka gano zai inganta ayyukanmu.

“Ina ba wa ma’aikatan lafiya kwarin gwiwa cewa kar su yi kasa a gwiwa domin har yanzu zutar tana nan.

“Ku yi amfani da kayan kariya yadda ya kamata; mun wadatar da cibiyoyin kula da lafiya da kayan kariyan”, inji shi.