Matasa ne suka fara kawo ci gaba a Najeriya – Kwamared Haruna

Wani matashi dan shekara 25 da ya fito takarar kujerar Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa maso Arewa a karkashin Jam’iyyar DA, Kwamared Haruna Yusuf Abba ya ce matasa ne suka fara kawo ci gaba a Najeriya. Kwamared Haruna ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin […]

Matasa ne suka fara kawo ci gaba a Najeriya – Kwamared Haruna

Kwamared Haruna Yusuf Abba

Wani matashi dan shekara 25 da ya fito takarar kujerar Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa maso Arewa a karkashin Jam’iyyar DA, Kwamared Haruna Yusuf Abba ya ce matasa ne suka fara kawo ci gaba a Najeriya.

Kwamared Haruna ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos. Ya ce sau tari mutanen Najeriya suna duban shekaru ne amma idan aka lura matasa ne suka fara kawo ci gaba a Najeriya. Ya ce yawancin shugabanninmu na baya a Najeriya, wadansu sun yi shugabanci ne suna da shekaru 22 zuwa 27 ne. Kuma sun samu nasarar kawo wa Najeriya gagarumin ci gaba, da har yanzu muke cin gajiya.

Ya ce idan wadancan shugabanni sun samu nasara a lokacin da suka yi shugabanci, lokacin da babu ilimi, me zai hana matasa su yi nasara a wannan zamani da ilimi ya yi yawa?

Ya ce don haka idan aka bai wa matasa dama a wannan lokaci, da yardar Allah za su yi abubuwan da za su kawo ci gaba a Najeriya.

“Yanzu idan ka dubi wasu kasashe da suka ci gaba a duniya, yawanci matasa ne suke mulkin kasashen. Kuma suna samun nasara saboda matashi ne yake da karfin jiki. Idan har yanzu a Najeriya, sai dai a ce matasa su je su jefa kuri’a ne kawai, su zabi wadanda ba za su taimaka musu ba, to babu wani ci gaba ga matasa a siyasar Najeriya,” inji shi.

Ya ce babban abin da ya karfafa masa gwiwar fitowa takara shi ne don ya ba da gudunmawarsa a matsayisa na matashi. Ya ce tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999 har zuwa yanzu babu wani abu na ci gaba da aka yi a wannan mazaba.

Ya ce al’ummar mazabar suna fama da matsalolin rashin ruwan sha da rashin kujeru da kayan aiki a makarantun gwamnati da rashin dakunan shan magani da kananan asibitoci da rashin aikin yi ga matasa da rashin tallafa wa mata masu sana’o’i a gidajensu da sauransu.

Ya ce idan Allah Ya sa ya yi nasara, zai yi amfani da kudaden da ake ware wa mazabu don warware wadannan matsaloli da suke damun mazabar. Kuma ya yi kira ga al’ummar mazabar su fito su kwansu da kwarkwata su zabi mutumin  da ya dace kuma ya cancanta a zaben da za a gudanar.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta