Matasa sun ba sojoji taimakon jini a Kamaru

A farkon makon nan ne mahukunta a kasar Kamaru suka yi shelar bukatar jini kimanin Lita dubu 190 domin taimaka wa dakarun kasar wadanda suka ji rauni sakamakon yaki da kungiyar Boko Haram.Babbar matsalar da ake fuskanta a asibitocin ita ce ta karancin jini da za a bai wa majinyata. Dangane da wannan ne wata […]

Matasa sun ba sojoji taimakon jini a Kamaru
Matasa sun ba sojoji taimakon jini a Kamaru

A farkon makon nan ne mahukunta a kasar Kamaru suka yi shelar bukatar jini kimanin Lita dubu 190 domin taimaka wa dakarun kasar wadanda suka ji rauni sakamakon yaki da kungiyar Boko Haram.
Babbar matsalar da ake fuskanta a asibitocin ita ce ta karancin jini da za a bai wa majinyata. Dangane da wannan ne wata kungiyar mai suna Majalisar Matasa  ta jagoranci mambobinta wajen ba da jini kyauta ga asibitin sojoji na birnin Yaounde. Wannan kamfen na ba da jini a fadin kakakin majalisar Jean Marc Afessi Mbafor zai gudana har zuwa lokacin da aka samu cinma buri wanda shi ne hada kan matasa 500 masu koshin lafiya wurin ba da wannan gudunmuwar.  Wani binciken da aka gudanar a kan adadin matasan da suka samu ba da jini da kuma ba a bayyana ba tukuna, ya tabbata cewa kashi 10 zuwa 13 na daukacin jinin da aka deba na kunshe da cutar kumburin hanta samfurin B wato (Hepatitis B). Har ila yau, kashi 5 kuma na dauke da kwayar cutar HIb mai haddasa  cutar nan mai karya garkuwar jiki.
Duk da cewa matasan sun ce suma suna fama da wasu matsaloli, amma sun gwammace sanyasu a gefe su tuna da wadanda suke filin daga, wadanda suke kare mutuncin kasa sakamakon bullowar hare-haren da yake hallaka rayukan jama’a. Kodayake, samun hada kan matasa guda 500 masu koshin lafiya ba abu ne mai sauki ba a fadin kakakin majalisar hadin kan matasan, amma kuma suna ci gaba da fadakar da su game da wannan muhimmin abu da zai shiga cikin tarihin ire-iren ababan da suke yi domin taimaka wa kasarsu ta haihuwa.