Matasa sun ceto sojan da ya yi yunkurin kashe kansa

Matasa sun kwashe sama da awa daya ana kokarin ceton ran wani tsohon soja da ya yi yunkurin kashe kansa a jihar Taraba. Tsohon sojan ya hau kan shataletalen shiga jihar Taraba mai tsawon kafa 24, mai dauke da rubutun ‘Barka da Zuwa Jihar Taraba’, ya yi yunkurin fadowa ya kashe kansa. Majiyarmu ta ce […]

Matasa sun ceto sojan da ya yi yunkurin kashe kansa

Sojojin Najeriya

Matasa sun kwashe sama da awa daya ana kokarin ceton ran wani tsohon soja da ya yi yunkurin kashe kansa a jihar Taraba.

Tsohon sojan ya hau kan shataletalen shiga jihar Taraba mai tsawon kafa 24, mai dauke da rubutun ‘Barka da Zuwa Jihar Taraba’, ya yi yunkurin fadowa ya kashe kansa.

Majiyarmu ta ce mutumin mai suna Ali tsohon soja ne kafin Rundunar Sojin Najeriya ta sallame shi bayan an lura yana da tabin hankali.

Matasan sun kewaye shataletalen suna ta rokon sa da kada ya fado, shi kuma yana cewa su  kyale shi ya fado ya mutu domin duniyar ta ishe shi.

Shaidu sun ce tsohon sojan wanda ke da rauni a kafa ya cire kayan jikinsa, ya rage daga shi sai dan kamfai da rigar singilet a jikinsa.

Ya yi ta yunkurin fadowa kasa kafin daga baya matasan su yi nasarar shawo kansa ya hakura ya sauko.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki