Matasa sun halaka dalibin jami’a a Malumfashi

A daren Lahadin da ta gabata ne al’ummar da ke zaune a kofar Fada Malumfashi, Jihar Katsina suka shiga jimami a yayin da wadansu matasa uku suka far wa wani matashi da bugu mai suna Abdulmalik Kabir, dan kimanin shekara 22 wanda ke zaune Titin Gidan Minista Malumfashi, wanda haka ya yi sanadiyar mutuwarsa. Mamacin, […]

Matasa sun halaka dalibin jami’a a Malumfashi

A daren Lahadin da ta gabata ne al’ummar da ke zaune a kofar Fada Malumfashi, Jihar Katsina suka shiga jimami a yayin da wadansu matasa uku suka far wa wani matashi da bugu mai suna Abdulmalik Kabir, dan kimanin shekara 22 wanda ke zaune Titin Gidan Minista Malumfashi, wanda haka ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Mamacin, wanda kafin rasuwarsa dalibi ne a Jami’ar Umaru Musa Katsina, kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, al’amarin ya faru ne a sanadiyar jan kunne tare da gargadin da shi marigayin ya yi wa daya daga cikin matasan uku, wanda kuma ake zargin shi ne ya gayyato su domin yi masa bugun kawo wuka. Matashin ya rasa hakoransa a lokacin da suke bugunsa, inda suka ingiza shi kasa, kansa ya bugi kwalta. An kwantar da shi a Babban Asibitin Malumfashi (kwandala), inda a nan ne ya rasu.

Aminiya ta ji ta bakin dan uwan mahaifin mamacin, Malam Bashir Haruna ta wayar salula. Ya ce su ne suka kai Abdulmalik asibiti a cikin wannan dare saboda ganin irin halin da yake ciki. Ya kara da cewa da farko magunguna ne aka fara rubuto masu suka saya amma ganin irin halin da yaron yake ciki ya sa suka mayar da shi asibitin. Sai dai ya ce tun lokacin da suka sake mayar da shi asibitin a cikin daren Lahadin. 

Malam Bashir ya ce Abdulmalik ya gamu da ajalinsa ne ta dalilin gargadi da ya yi wa wani matashi mai suna Husaini Abdullahi danshagamu, mazaunin Layin Lamarudu Malumfashi. Inda ya ce masa ya daina kiran kanwarsa a waya da sunan wai yana sonta. “Abdulmalik ya gargadi Husaini ba sau daya ba, a kan ya daina kiran Amira ’yar kimanin shekara 17, domin ba a tashi yi mata aure ba a yanzu saboda karatu da take yi amma Husaini ya ki jin wannan gargadin. A iya saninmu, wannan shi ne dalilin rashin jituwarsu har ta kai ga faruwar wannan al’amari,” inji shi.

Shi kuwa Abba wanda aboki ne na kusa ga Abdulmalik ya ce: “Muna zaune tare da marigayi a daren Talata, sai Amira ta sake yi wa shi Abdulmalik koken irin matsa mata da shi Husaini ke yi da kiran waya, ta ce har ya fara sa wa ta fara shiga cikin wani yanayi. To sai a ranar Laraba na ga shi Abdulmalik ya yi zaune shiru cikin tunani.

“Da farko ya ki ya gaya mani abin da yake tunani, sai da ya ga na bata rai sannan yake gaya mani batun Husaini ne da Amira. Nan gabana ya sake kiran Husaini don yi masa gargadi na karshe, wanda hakan ya sa har shi Husainin yake cewa babu wanda ya isa ya hana shi yin soyayya da Amira, ko ya hana ya kira ta. Har ma ya kara da cewa, in shi Abdulmalik ɗa ne ya fito su hadu a wannan lokacin. Ni na hana shi fita, inji Abba.

Ya ci gaba da cewa, a daren Lahadin da ta gabata ce marigayin ya je kofar Fada wajen wasu abokansa, inda shi Husaini da abokansa biyu da ake kira da lakanin Kwaso dan unguwar kofar Fada da kuma wani Bayarabe da ake kira Lakazir dan Unguwar Sodangi suka far masa da bugu. Ya ce: “An yi kokarin shiga tsakani amma sai wani daga cikinsu ya biyo ta baya ya buga shi da kasa, kansa ya bugi kwalta har hakoransa suka burma a ciki. Ganin haka ya sa suka gudu, shi kuma aka kai shi asibiti. Amma sai a wajen karfe 10 na safiyar Litinin ya mutu.”

Aminiya ta tuntubi Kakakin ’yan sanda a Jihar Katsina DSP Gambo Isa don jin ta bakinsu. Ya tabbatar da faruwar haka, inda ya ce sun yi nasarar kama Husaini dan shekara 22 tare da Abdul’aziz Abubakar da kimanin shekara 20, inda ake kan bincike. Ya ce suna cikin neman matashi na uku, domin gurfanar da su gaban shari’a.