Matasa sun haramta shan wiwi a Bauchi
A kokarinsu na tabbatar da cewa an magance matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, Kwamitin Gyara Tarbiyyar Matasa na Unguwar Bakin Kura da ke garin Bauchi ya haramta shan tabar wiwi a unguwar baki daya.Da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa Malam Abubakar dandada kuma daya daga cikin dattawan da suke […]
A kokarinsu na tabbatar da cewa an magance matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, Kwamitin Gyara Tarbiyyar Matasa na Unguwar Bakin Kura da ke garin Bauchi ya haramta shan tabar wiwi a unguwar baki daya.
Da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa Malam Abubakar dandada kuma daya daga cikin dattawan da suke aiki da kwamitin ya ce saboda yadda aka shafe sama da shekara 30 ana hada-hadar tabar wiwi a unguwar a halin yanzu da yawa daga cikin masu sana’ar saida tabar sun tuba.
Don haka aka kafa kwamitin gyara tarbiyyar matasa na jihar baki daya.
Malam dandada ya ce kasha 85 cikin 100 na unguwannin garin Bauchi sun amfana da kafa kwamitin don haka ya yi kira da babban murya ga al’umma su kafa makamancin wannan kwamiti.
Alhaji Muhammed Malami Sakkwato shi ne sabon Shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi (NDLEA) ya shaida wa wakilinmu cewa ya ji dadi sosai lokacin da ya samu labarin cewa mutanen Bakin Kura sun kafa kwamitin haramta shan tabar wiwi.
Ya ce a matsayinsa na sabon shugaban hukumar zai ci gaba da wayar da kan al’umma ta yadda za su nisanci sha da fataucin miyagun kwayoyi.