Matasa sun harbi ma’aikatan Kamfanin Simintin Dangote a Kogi

Matasan Jihar Kogi sun harbi ma’aikatan kamfanin saboda rashin yarda da mallakar masana’antar

Matasa sun harbi ma’aikatan Kamfanin Simintin Dangote a Kogi

An harbi ma’aikata da dama a Kamfanin Simintin Dangote da ke Obajana a Jihar Kogi da bindiga bayan wasu matasa sun kai wa kamfanin farmaki.

A safiyar Laraba daururwan matasa dauke da makamai suka yi wa masana’antar simintin dirar mikiya karkashin jagorancin manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kogi.

Rahotanni sun nuna bayan matasan da jami’an gwamnatin jihar sun yi dafifi a harabar kamfanin ne aka yi samu cacar baka tsakaninsu da jami’an tsaron da ke gadin kamfanin.

Wani dan garin ya ce sun yi ta jin karar harbi a safiyar ranar Laraba, wanda hakan ya sa mutane suka yi ta guje-guje.

Sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce mutane fiye da 500 dauke da makamai iri-iri, na gida da na zamani, sanye da kayan kungiyar tsaron jihar ne suka far wa masana’antar.

Ta ce an harbi ma’aikatan kamfanin da dama a hatsaniyar, tuni kuma aka kai su asibiti domin yi musu magani.

Sanarwar ta ce “Bijilantin sun shigo ne karkashin jagorancin Babban Daraktan Lura da Filaye da kuma Kwamishinan Ma’adanai da Babban Hadimin Gwamna na Musamman Kan Harkokin Tsaro da Commodore Jerry Omodara (mai ritaya), sai Shugaban Karamar Hukumar Kabba/Bunnu.

“Sauran sun hada da Shugaban Karamar Hukumar Ijumu, da Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) na jihar, Alhaji Taofeek da Babban Hadimi na mMusamman kan Samar da Ayyuka, Mista Dele Iselewa, da sauransu.”

A martaninta, Gwamnatin Jihar Kogi ta ce matasan sun fatattaki ma’aikatan Kamfanin Simintin Dangote da ke Obajana, kuma gwamnatin jihar ta rufe masana’antar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran jihar, Kinsley Fanwo, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta rufe masana’antar ne bayan korafe-korafen da ’yan jihar ke sanya ayar tambaya kan halascin mallakar kamfanin.