Matasa sun jefi jami’an tsaro bayan rantsar da sabon Gwamnan Kano

Matasa n dai sun yi yunkurin shiga gidan gwamnati ne amma aka hana su

Matasa sun jefi jami’an tsaro bayan rantsar da sabon Gwamnan Kano

Kofar Gidan Gwamnatin Kano

Wasu fusatattun matasa sun yi ruwan duwatsu ga jamian tsaro a kan hanyar Gidan Gwamnatin Kano, bayan da aka hana su karasawa ciki.

A ranar Litinin ce dai aka rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon Gwamnan Jihar, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Dubun-dubatar mutane ne suka yi tururuwa zuwa wajen bikin rantsuwar, inda daga bisani da yawa daga cikinsu suka yi kokarin shiga gidan gwamnati, amma jami’an tsaro suka hana su.

Wani da lamarin ya fara a kan idonsa ya shaida wa Aminiya cewa matasan sun fara jufan jami’an tsaron ne bayan sun hana su karasawa gidan gwamnati don tarbar sabon Gwamnan da aka rantsar.

“’Yan sanda da sojoji ne suka taso mu a gaba wai sai mun juya ba za mu shiga ba. Shi ne wasu suka fusata suka hau jifa da duwatsu,” in ji shi.

Rahotanni na nuna cewa jami’an tsaron sun hana matasan shiga ne duba da yawansu, da kuma fargabar batagari za su yin amfani da damar wajen tayar da hankali.

 

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda