Matasa sun jefi Shugaban Majalisar Sakkwato saboda hare-haren ’yan bindiga

Wakilinmu ya ziyarci garin Bodinga, inda ya tarar da daruruwan ’yan gudun hijira suna neman mafaka a makarantu, masallatai da gidajen jama’a.

Matasa sun jefi Shugaban Majalisar Sakkwato saboda hare-haren ’yan bindiga

Matasa sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a, bayan sakamakon tashin hankali da al’umma suka shiga bayan sabbin hare-haren ’yan bindiga da suka tilasta mazauna kauyuka barin gidajensu a Karamar Hukumar Bodinga ta Jihar Sokoto. 

Wakilinmu ya ziyarci garin Bodinga, inda ya tarar da daruruwan ’yan gudun hijira suna neman mafaka a makarantu, masallatai da gidajen jama’a.

Matasa da dama sun toshe babban titin Sokoto–Yauri–Birnin Kebbi, suna neman gwamnatin jihar ta gaggauta kawo karshen hare-haren da suka zama ruwan dare. 

Masu zanga-zangar sun kunna wuta a kan titin tare da tare hanyar da itatuwa, lamarin da ya jawo cunkoson ababen hawa na tsawon sa’o’i, kafin jami’an tsaro su tarwatsa su da misalin ƙarfe 12 na rana.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa zanga-zangar na nufin jawo hankalin hukumomi kan tabarbarewar tsaro. 

Shaidu sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Tukur Bala Bodinga, ihu tare da jifa da duwatsu a lokacin da ya isa wajen, sai dai ba a lalata motoci ba.

“Ba za mu ci gaba da yin shiru ba alhali ana kashe mutanenmu kuma ana tilasta musu barin gidajensu. Yanzu da dama sun nemi mafaka a Bodinga saboda ba su da inda za su je,” in ji wani mazaunin yankin.

Aminiya ta iske mata da yara da tsofaffi daga kauyuka daban-daban suna neman mafaka a wurare kamar Makarantar Alhaji Sahabi Bodinga, Makarantar Dan Jeka, Makarantar Liman, Masallacin Mallam Bala, sabon kasuwa a Bodinga da kuma garin Sifawa. 

A Sifawa, Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto, Muhammad Bello Sifawa, ya ba da gidansa don saukar da ’yan gudun hijira.

Wani daga cikin ’yan gudun hijira daga kauyen Qyaula ya ce ’yan bindiga sun shigo kauyen da yammacin Alhamis suna harbi ba kakkautawa, inda suka kashe wasu, kafin jama’a su tsere. Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Qyaula, Keloji, Chohi Takule, Kulodo, Kwamtsi, Danchadi, Lugge, Dabagi da Karaje.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun ratsa kauyukan ne daga misalin karfe 2 na rana har zuwa safiyar Juma’a, suna kashe mutane da tilasta wa jama’a barin gidajensu. 

Daga bisani, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Tukur Bala Bodinga; dan majalisar wakilai, Nasiru Shehu Bobo; Sakataren Gwamnatin Jihar, Muhammad Bello Sifawa; Shugaban Karamar Hukumar Bodinga; hakimi da jami’an tsaro sun ziyarci yankin don jajanta wa al’umma tare da halartar jana’izar wadanda aka kashe.

Mai magana da yawun ’yan sanda na jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, ya ce jami’an tsaro sun yi aiki a yankin tun daga yammacin Alhamis har zuwa ƙarfe 3 na safiyar Juma’a, kuma an kara tura karin jami’ai don tabbatar da tsaro. 

Ya roki jama’a da su guji toshe manyan hanyoyi duk da koke-kokensu.

An riga an gudanar da jana’izar mutanen da aka kashe a Lugge. 

Wannan hari ya zo kwana daya bayan da aka kashe Babban Limamin Talluje da wasu mutum biyu a Bodinga, abin da ya kara nuna tsanantar matsalar tsaro a yankin.