Matasa sun kashe dan kunar bakin wake a Gombe
A ranar Talatar da ta gabata ne wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin shiga tashar mota ta Gombe Line dauke da bam amma bai yi nasara inda wasu matasa suka cafke shi suka kone shi kurmus. Matashin wanda ya yi niyyar shiga tashar a matsayin fasinja dauke da jaka a baya, inda jami’an […]
A ranar Talatar da ta gabata ne wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin shiga tashar mota ta Gombe Line dauke da bam amma bai yi nasara inda wasu matasa suka cafke shi suka kone shi kurmus.
Matashin wanda ya yi niyyar shiga tashar a matsayin fasinja dauke da jaka a baya, inda jami’an tsaro suka nemi ya bayar don a bincika amma ya ki.
Wani ganau da ya ce a sakaye sunansa ya shaida wa manema labarai cewa an bukaci matashin ya bayar da jakarsa a duba saboda halin tsaro, amma sai ya ce ba zai bayar ba, ya sa kai zai shiga tashar da karfi aka hana shi.
Majiyar ta ce dan kunar bakin waken ya sake sa kai zai wuce cikin tashar da karfin tsiya ba tare da an duba ba, shi ne jami’an tsaron suka hana shi, sai ya fara neman yin fada da su, inda wasu matasa suka taso masa ya jefar da jakar zai gudu aka bishi aka kama shi.
Ya ce da aka duba jakar ne sai aka ga ashe bam ne a ciki, sai matasan suka rike shi suka yi ta duka har ya mutu sannan suka sanya masa taya suka banka masa wuta ya kone kurmus a wajen tashar ta Gombe Line, kuma suka ce ba za su bar wurin ba har sai ya zama toka.
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan lamarin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Abdullahi Kudu Nma, ya ce da wannan dan kunar bakin wake ya yi nasarar shiga tashar ya tada bam din da zai yi barna sosai kamar wanda ya faru mako hudu da suka wuce.
Kwamishinan ya yaba da yadda jami’an tsaron suke gudanar da aikinsu na duba kayan fasinja kafin su shiga tashar, inda ya ce kafin ya isa wurin, matasan an kashe dan
kunar bakin waken.
Idan za a iya tunawa a ranar 31 ga Oktoba mahara sun tada wani bam a wannan tashar inda ya halaka fiye da mutum 22 wasu fiye da 40 suka samu munanan raunuka.