Matasa sun kashe Kofur din da ya kashe matashi a Gombe
A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu hatsaniya tsakanin wani dan sanda mai mukamin Kofur mai suna Adamu Abba da wani mai Keke NAPEP a unguwar Tudun Wada da ke Gombe fadar jihar, inda dan sandan ya harbe wani matashi da ya zo rabiyar fada mai suna Mala Gana lamarin da ya tunzura […]
A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu hatsaniya tsakanin wani dan sanda mai mukamin Kofur mai suna Adamu Abba da wani mai Keke NAPEP a unguwar Tudun Wada da ke Gombe fadar jihar, inda dan sandan ya harbe wani matashi da ya zo rabiyar fada mai suna Mala Gana lamarin da ya tunzura matasa suka kashe dan sandan.
Al’amarin ya faru ne da safe lokacin da dan sandan ya fito zai tafi aiki a barikinsu na Mobile da ke hanyar Kwami, inda bisa kuskure mai Keke NAPEP din ya kade dan sandan da ke kan babur har bindigarsa ta fadi.
Wani da abin ya faru a kan idonsa, kuma ya nemi a sakaye sunansa ya ce dan sandan ne ba ya da gaskiya domin ba a kan hannunsa yake ba a lokacin da mai Keke NAPEP din ya kade shi amma duk da haka an ba shi hakuri ya ki, ya ce sai an biya shi babur dinsa.
Majiyar ta ce a lokacin da ake ba shi hakurin ne ya fara harbi a sama don ya tsorata mutane, ganin haka sai mutan suka fara gudu, inda ya nufi inda Keke NAPEP din take yana cewa sai an biya shi kafin. “Kafin ka ce me mutane sun sake taruwa a nan ne Mala Gana ya zo yana kokarin ba dan sandan hakuri shi ne sai ya daga bindiga ya harbe shi ya mutu. Ganin ya mutu ne sai jama’a suka fara biyo shi daga inda hadarin ya faru a kusa da gidan marigayi Alhaji Baba Manu (ABM), yana gudu yana harbi a sama har harsashinsa ya kare sai ya fada ofishin sakataren Sarkin Gombe don neman tsira amma jama’a suka bi shi suka kamo shi suka kashe shi,” inji majiyarmu.
Da manema labarai suka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Fwaji Atajiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce jama’a sun yi kuskure wajen daukar doka a hannunsu wajen kashe dan sandan maimakon su yi bincike a kan abin da ya faru.
DSP Attajiri, ya ce a lokacin da mai Keke NAPEP ya kade dan sandan bindigarsa ta fadi a nan ne ta zama ta danu bai sani ba da jama’a suke kokarin kwace masa bindigar shi ma yana ja a nan ne kunamar bindigar ta tashi ta kashe matashin ba da son ransa ba ganin haka ne ya sa tun daga nan ya sake rufe ta ba tare da ta sake yin harbi ba su kuma zauna gari banza suka yi ta dukan dan sandan har suka kashe shi.
Kakakin ’yan sandan ya ce idan abu irin wannan ya faru jama’a su daina saurin daukar doka a hannunsu su tsaya su bincika. Sai ya yi kira ga al’umma su zamo masu hakuri su rika tsayawa suna bincike kafin daukar kowane irin mataki.
Kofur Adamu Abba, yana da shekara 38, shi kuma Mala Gana wanda dan Unguwar Tudun Wada ne yana da shekara 37.