Matasa sun kashe magidanci don ya hana su fyade

Ana zargin wadansu matasa uku a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa masu suna Aminu da ake kira danjummai Maikifi da Iliya da kuma Muhammed Lawan da halaka wani magidanci mai suna Nasiru Ya’u saboda zargin zai tona musu asiri bayan da ya haska su da tocila a lokacin da suke kokarin yi wa wata […]

Matasa sun kashe magidanci don ya hana su fyade
Matasa sun kashe magidanci don ya hana su fyade

Ana zargin wadansu matasa uku a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa masu suna Aminu da ake kira danjummai Maikifi da Iliya da kuma Muhammed Lawan da halaka wani magidanci mai suna Nasiru Ya’u saboda zargin zai tona musu asiri bayan da ya haska su da tocila a lokacin da suke kokarin yi wa wata yarinya fyade.
Matasan wadanda ’yan sanda ke nemansu zuwa hada wannan rahoto sun halaka Nasiru Ya’u ne mai shekara 34 a ranar Alhamis din makon jiya a Unguwar Makafi a Tsohon Kafi a garin Kazaure.
Mijin mahaifiyar marigayin mai suna Malam Is’haka Adamu ya shaida wa wakilinmu a Kazaure cewa matasan sun isa wurin da Ya’u a bakin masallacin unguwar suka kama
kokawa da shi ne a lokacin babu wanda ya san laifin da marigayin ya yi musu sai jama’a suka shiga tsakani suka ba su hakuri. “Ashe ba su hakura ba da tsakar dare yana kwance a bakin masallaci sai aka ji kururuwarsa yana neman taimako saboda matasan sun sake dawowa a kan babur sun fada shi da sara, kafin jama’a su kai agaji sun sare masa wuyan hannu, sun bar shi cikin jini kace-kace,” inji shi.
Ya ce ya garzaya da Ya’u zuwa asibitin Kazaure bayan ya samu taimakon ’yan sanda amma ana kokarin kara masa jini sai ya cika aka dawo da shi gida aka yi masa sutura.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Mai Unguwar Tsohon Kafi Malam Isyaku Abdu
ya ce labarin haka yake amma babban kuskure da mijin mahaifiyar yaron ya yi bai sanar da shi ba.
Mai unguwa Isyaku Abdu ya ce matasan da suka aikata kisan an san su an san mahaifansu,  mazauna Unguwar Barga ne (Sha’iskawa), ya ce tuni suka sanar da ’yan sandan Kazaure.
Wani mazaunin unguwar da aka aka sakaye sunansa ya ce matasan sun halaka Ya’u ne saboda  kada ya tona musu asiri saboda ya haska su a lokacin da suke kokarin yi wa wata yarinya fyade a kusa da makwabtansa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa DSP Abdul Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rundunar tana neman wadanda suka aikata kisan gillar, kuma da zarar an kama su za su gabatar da su a gaban kotu domin hukunta su.