Matasa sun kashe ’yan bindiga a Sakkwato

Matasan gari sun kashe ’yan bindiga uku, cikinsu har da mace, bayan an cafke ’yan bindigar.

Matasa sun kashe ’yan bindiga a Sakkwato

Mutanen gari sun kashe ’yan bindiga uku, cikinsu har da mace, bayan sun yi artabu da ’yan bindigar a Jihar Sakkwato.

Fusatattun matasa sun yi wa ’yan bindigar kisan gilla ne bayan macen da aka kama ta yi burgar cewa ta san babu abin da za a yi mata.

’Yan bindigar sun kai hari ne a wata rugar Fulani ranar Laraba da dare suna kokarin satar shanu, amma ’yan kauyen suka fito yi fito-na-fito da su, suka fatattake su, suka kama uku daga cikinsu, suka mika wa ’yan banga.

Wani shaida ya ce mutanen “A shirye suke, Sun kama ’yan bindiga uku, cikinsu har da wata mace, da gari ya waye sai suka mika su a hannun ’yan banga.”

Ya ci gaba da cewa “Da matasan gari suka samu labari, sai suka yi dandazo a ofishin ’yan bangar da ke a garin Goronyo.

“Abin da ya fusata si shi ne irin gadarar da macen da ke cikin ’yan bindigar take yi cewa an sha kama ta kuma ana sakin ta, saboda haka ta san wannan karon ma sakin ta za a yi.

“Abin da ya fusata su ke ke nan, har suka fi karfin ’yan bangar suka banka wa ofishin ’yan bangar wuta.

“Daya dan bindigar ya mutu ne a cikin ofishin ’yan bangar da ke ci da wuta, ita macen da dayan kuma sun yi kokarin fita ta taga su tsere, amma aka kama su, aka kashe su, aka kona gawarsu kurmus,” inji shi.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, amma a lokacin da muka tuntube shi ya ce ba shi da cikakkun bayanai.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Abdulwahab Yahya ce an tura jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda.

Ya bayyana cewa duk da jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma 60 da aka girke kauyen, ’yan bindiga sun ci gaba da zuwa suna satar dabbobi.

“Ko kwanaki biyu da suka wuce sai da aka sace dabbobi da misalin karfe 7 na yamma a kusa da Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke daura da Masaukin Gwamna, inda aka yi wa ’yan sandan kwantar da tarzoma masauki.

“Mutane sun gaji da abubuwan da ke faruwa. Suna ganin kokarin da muke yi ya gaza, shi ya sa suke daukar doka a hannunsu,” inji shi.

Abdulwahab ya kara da cewa hukumomin tsaro sun fara bincike kan al’amarin.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC