Matasa sun kona mota 6 kan sauya wa gidan dirama matsuguni a Maraba
Wadansu matasa da ke zanga-zangar sauya wa ’yan dirama matsuguni daga garin Marabar Guruku zuwa kauyensu na Aso-Pada da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa sun kona motoci 6 da suka hada da tifofi. Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a shekaranjiya Laraba ya samu labarin cewa filin da ’yan tifa ke amfani da shi […]
Wadansu matasa da ke zanga-zangar sauya wa ’yan dirama matsuguni daga garin Marabar Guruku zuwa kauyensu na Aso-Pada da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa sun kona motoci 6 da suka hada da tifofi.
Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a shekaranjiya Laraba ya samu labarin cewa filin da ’yan tifa ke amfani da shi a baya da ke daura da babban titin Abuja zuwa Keffi da aka fi sani da Gidan-Soja, gwamnatin jihar ce ta ba su a matsayin matsuguni kafin daga bisani sauran al’umma da suka hada da ’yan dirama da gidajen dambe suka kutsa cikinsa.
Wani direban tifa da ya zanta da Aminiya ya ce gwamnatin ta bukaci wajen a yanzu da nufin kafa tashar mota ta zamani. “Mun bi umarninta a ranar Lahadin da ta gabata zuwa sabon filin da ta ba mu a Aso-Pada, sai kawai matasan kauyen suka auka mana, sun kona mana motoci 6 da kuma raunata yaranmu 16 ta hanyar saransu da makami,” inji shi.
Wakilinmu ya ziyarci gidan hakimin kauyen, sai dai an sanar da shi cewa ya je garin Lafiya babban birnin jihar a ranar, inda aka gayyace shi a kan lamarin.
Sai dai wani shugaban al’umma a yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ta’allaka al’amarin da matsalar rashin tuntuba a tsakanin shugabannin garin da hukuma, inda ya ce ba ta sanar da su shirin dawo da ’yan tifa zuwa yankin ba.
Haka ya ce ba a biya diyya ga ainihin masu filin ba, ga kuma fargabar da ya ce wasunsu ke ji na dawowar ’yan dirama zuwa kauyen kan za ta gurbata tarbiyyar iyalansu.
Babban Jami’in ’Yan sandan Maraba “A” C.P Muhammad Padah wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ya mika rahoton abin ga babbar hedikwatarsu da ke Lafiya.