Matasa sun lakada wa Barman Gumel duka kan kudin TAN
Matasa da ke goyon bayan kungiyar yada manufofin Shugaba Jonathan (TAN) a Jihar Jigawa da aka kira su taro da nufin ba su takardun da za su cike a dauke su aiki tare da ba su tallafin kudi sun yi wa shugaban SURE-P jihar, Malam Yusif Alhasan Barman Gumel duka har sai da jami’an tsaro […]
Matasa da ke goyon bayan kungiyar yada manufofin Shugaba Jonathan (TAN) a Jihar Jigawa da aka kira su taro da nufin ba su takardun da za su cike a dauke su aiki tare da ba su tallafin kudi sun yi wa shugaban SURE-P jihar, Malam Yusif Alhasan Barman Gumel duka har sai da jami’an tsaro suka kwace shi.
Lamarin ya kai har an karya dan sandan da yake ba shi kariya mai suna Ibrahim a hannu lokacin da yake kokarin kare lafiyarsa daga matasan.
Matasan sun yi zargin cewa Barman na Gumel ya jima yana yaudararsu, inda wata majiya ta ce a kwanakin baya ya gayyatosu daga kananan hukumomin jihar 27, amma bai ba su koda sisin kwabo ba, lamarin da ya sa aka tashi baram-baran.
Majiyarmu ta ce a wannan karon an sake tara matasan daga kananan hukumomin jihar a karkashin kungiyaar TAN inda wasu da ake zargin ’yan kabilar Ibo ne suka zubar da su a cibiyar horar da matasa tun karfe 12:00 na rana har karfe 5:00 na yamma ba wanda ya ce musu komai, lamarin da ya harzuka matasan suka huce fushinsu a kan shugaban na SURE-P.
Shugaban kwamatin matasa masu fafutikar a sake zaben Shugaba Jonathan na jihar Malam Aminu Aminu, ya ce da kyar aka kwace su daga hannun matasa domin matasan sun fara yunkurin farfasa masa mota har sun fara dukanta suna karya ne ba ma yi, ba ma so Najeriya sai Buhari, kan ya samu ya tsallake.
Aminu ya ce da matasan sun san abin da ke faruwa da ba su daki Barman na Gumel ba, domin duk kudin da ake turowa daga Gwamnatin Tarayya a ba su su taimaka wa matasan da nufin yada manufofin Shugaba Jonathan ba sa zuwa hannunsu, “hakan ya sa Barman ba ya iya yin komai sai ya rubuta wa ofishin Gwamna,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa DSP Abdu Jinjiri ya ce ba su samu labarin aukuwar lamarin ba, amma idan ya samu bayani zai sanar da halin da ake ciki.