Matasa sun lalata motocin ‘yan sanda 3 a shagon Shoprite na Abuja
Wasu matasa sun lalata motocin ‘yan sanda uku a lokacin da suka yi yunkurin shiga shagon siye da siyarwa na Shoprite da ke Alieta hanyar Airport road a Abuja. Matasan dai sun taru ne da yawa a tsakanin gadar unguwar Lugbe zuwa Alieta wanda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a hanyar. Wakilin mu da […]
Wasu matasa sun lalata motocin ‘yan sanda uku a lokacin da suka yi yunkurin shiga shagon siye da siyarwa na Shoprite da ke Alieta hanyar Airport road a Abuja.
Matasan dai sun taru ne da yawa a tsakanin gadar unguwar Lugbe zuwa Alieta wanda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a hanyar.
Wakilin mu da ya ziyarci wurin da abin ya faru, ya ce matasan na dauke da duwatsu a hannuwan su inda suka rika jifan motocin ‘yan sandan tare farfasa gilashen motocin matafiya a hanyar.