Matasa sun qone ’yan fashi qurmus a Jihar Nasarawa

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu matasa a Lafiya fadar Jihar Nasarawa suka yi wa wasu ’yan fashi biyu danyen hukunci, inda suka qone su da wuta qurmus. Lamarin ya auku ne a hanyan Lafiya zuwa Jos kusa da bankin Stanbic IBTC da misalin qarfe 2:30 na rana. Wani daga cikin wadanda lamarin […]

Matasa sun qone ’yan fashi qurmus a Jihar Nasarawa
Matasa sun qone ’yan fashi qurmus a Jihar Nasarawa

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu matasa a Lafiya fadar Jihar Nasarawa suka yi wa wasu ’yan fashi biyu danyen hukunci, inda suka qone su da wuta qurmus.
Lamarin ya auku ne a hanyan Lafiya zuwa Jos kusa da bankin Stanbic IBTC da misalin qarfe 2:30 na rana.
Wani daga cikin wadanda lamarin ya auku kan idonsu da ya buqaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, ’yan fashin su biyu sun qwace Naira dubu 400 ne daga hannun wani mutum da ya fito daga bankin First Bank da ke nan hanyar Jos. Kuma suna yunqurin tsallake hanya ne sai wata qaramar mota qirar Gulf ta buge su.
Ya ce, “Faduwarsu ke da wuya sai wasu sojoji da ke kusa suka soma lakada musu duka daga bisani matasan da suka yi cincirindo suka kama dukansu suka kuma cinna musu wuta.”
Wakilinmu ya lura daya daga cikin ’yan fashin ya qone qurmus a yayin da dan uwansa ’yan sandan da suka iso wurin suka yi qoqarin ceto shi, inda aka kai shi Asibitin Qwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya don ceto ransa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Norman Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ’yan fashin sun biyo mutumin ne har bankin inda suka jira ya cire kudinsa suka qwace kafin dubunsu ta cika. Ya ce tuni rundunar ta fara bincike a kan lamarin. Qoqarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin wanda aka kwace masa kudin ya citura kasancewa ’yan sanda da suka isowurin sun kai shi ofishinsu don ci gaba da bincike a kan lamarin.