Matasa sun raunata soja bayan kashe mai sayar da takalmi a Kaduna
Wasu matasa cikin fushi sun raunata wani soja bayan an zarge shi da kashe wani matashi mai sayar da takalmi a kasuwar Shaikh Gumi da ke Kaduna. Lamarin ya auku ne a yau Alhamis da misalin karfe 2:30 na rana. An bayyana sunan matashin da Yusuf, sai dai ba a sanar da dalilin da yasa sojan […]
Wasu matasa cikin fushi sun raunata wani soja bayan an zarge shi da kashe wani matashi mai sayar da takalmi a kasuwar Shaikh Gumi da ke Kaduna.
Lamarin ya auku ne a yau Alhamis da misalin karfe 2:30 na rana.
An bayyana sunan matashin da Yusuf, sai dai ba a sanar da dalilin da yasa sojan ya daba masa wukar ko da wa ake hatsaniyar da ta yi sanadiyar mutuwarsa.
Wani magidanci mai suna Salis, wanda ya shaidawa wakilinmu abin da ya faru ya ce, su dai kurum sun ji an ce ga soja can ya kashe wani.
“Muna zaune sai muka ga ana gudu wai soja ya cakawa mai sayar da takalmi wuka a kirjinsa. Su kuma sauran matasa da ke wurin suka hau sukan sojan da karafa da sanduna har suka raunata shi kafin daga bisani aka dauke shi.” In ji shi.
Jami’an tsaro sun yi tururuwa zuwa wurin da abin ya faru wanda hakan yasa jama’a suka rika gudu.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan jihar Yakubu Sabo, ya ce zai bincike lamarin kafin ya ce wani abu.