Matasa sun rushe makarantar masu akidar cin naman kare a Kaduna
Matasa sun rusa gida da makarantar wani malami da ya jagoranci dalibansa suka ci naman kare a Jihar Kaduna.
Matasa sun rushe gida da makarantar wani malami da ya ci naman kare tare da dalibansa a unguwar Nassarawa a Jihar Kaduna.
Cin naman karen da mutum da almajiransa suka yi ranar Talatar nan da ta gabata ya fusata matasan unguwar suka yi zanga-zanga tare da rusa gidan wanda ake zargin.
- Iftila’i: Ya kamata ’yan Najeriya su taimaka wa Morocco da Libya —Malamai
- NAJERIYA A YAU: Yadda karewar hutun makarantu ya gigita iyaye
Aminiya ta gano cewa ainihin wanda ake zargi da yanka karen ya tsere, tun bayan da labarin ya bazu a gari.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sadan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunar tana binciken.
Sai dai a cewarsa, wanda ake zargin ya ce bai yanka karen saboda suna da aka yi masa ba, kamar yadda ake yadawa. Amma ya ce, addininsu ya yarda da haka kuma a cewarsu ba su saba wa addinin da suke bi ba.
Daya daga cikin mabiya akidar halasta cin naman kare a unguwar da bai ambaci sunansa ba ya ce, shaida wa manema labarai cewa, “Mu fa Musulmai ne da muka yarda da littafin Al’kurani a matsayin littafin ibada. Kuma da Alkur’aini muke ibada. Ibadanmu ya sha bamban da na sauran mutane.
“Kuma Najariya kasa ce da ta bai wa kowa ’yancin yin addininsa kuma a iya fahimtarmu, babu inda Allah Ya hana a ci kare.
“Sai muka ce duk wanda ya ce an saba mishi ko an saba wa Allah, toh ya kawo mana ayar, idan muka gani muka fahimta sai mu roki Allah gafara mu daina.”
A cewarsa, su ba yan ta’adda ba ne domin ba sa zagin kowa kuma su masu biyayyane ga gwamnati. Ya kuna nemi malamai su fito su fada masu kuskurensu domin su gyara.
Kakakin ’yan sandan jihar ya ce, “Amma muna nan muna bin cike a kai domin sanin akidar da suke bi. Sun ce wai su Al’kurani suke bi sak. Mun kuma bincike su an san iyayensu amma kuma sun zo suna wannan akida,” in ji shi.
Ya ce rundunar ba zata yarda wasu mutane su kawo rudani ba akasa ba duk da cewa dokar kasa ta baiwa kowa yancin yin addininsa.