Matasa sun shirya walima don Buhari

Kwamitin matasa masu wa’azi na kungiyar Izala ta kasa reshen Jihar Kurosriba da ke kalaba ya shirya walima domin nuna farin ciki tare da murnar canji da aka samu na shugabanci a kasar nan. Da yake hira da Aminiya dangane da makasudun shirya walimar, sakataren kwamitin da ya shirya walimar, Malam Musa Salihu dantagada ya […]

Matasa sun shirya walima don Buhari
Matasa sun shirya walima don Buhari

Kwamitin matasa masu wa’azi na kungiyar Izala ta kasa reshen Jihar Kurosriba da ke kalaba ya shirya walima domin nuna farin ciki tare da murnar canji da aka samu na shugabanci a kasar nan.

Da yake hira da Aminiya dangane da makasudun shirya walimar, sakataren kwamitin da ya shirya walimar, Malam Musa Salihu dantagada ya bayyana cewa sun yi haka ne domin su gode wa Allah da kuma yi wa sabuwar gwamnati fatar alheri.
Da yake karin haske game da walimar, Malamin ya ci gaba da cewa: “Alal hakika mun shirya wannan walima ce bisa koyarwa ta Manzon Allah (saw), inda ya koya mana cewa duk wani Musulmi da Allah Ya yi wa baiwa ta aure ce, ko ta haihuwa manzo ya kwadaitar da mu cewa mu yi walima da abin da Allah Ya huwace mana, ba wai sai lallai da tarin abu mai yawa ba kuma ya kwadaitar da sahabbansa idan wata ni’ima ta same su, to su yi walima domin godiya ga Allah (swt).”
Da Aminiya ta tambaye shi ko kungiyarsu na da alaka da siyasa? Sai ya yi karin haske da cewa: “Gaskiya ba ta da alaka da siyasa. Wannan kungiya tamu babu wata kungiyar siyasa da take daukar nauyinmu, duk abin da ka ga mun yi kungiyar Izala ce kuma karkashinta muke komai tsakaninmu ne muke tara kudin mu biya bukatunmu na daukaka addini ko yi masa hidima. Sai dai gudunmawa kan shigo daga daidaikun al’ummar Musulmi amma ba ruwanmu da siyasa kuma babu wani dan siyasa da ke daukar nauyinmu. Mu ma ba za mu yarda da hakan ba, ba kuma za mu so hakan ba.”