Matasa sun so yin rajamu ga ’yan luwadi a Bauchi
Matasan da suka halarcin zaman shari’ar wadanda ake zargi da aikata luwadi a Bauchi sun fusata inda suka nemi yin rajamu ga wadanda ake zargin, lamarin da ya sanya alkalan kotuna biyu da ke shari’ar wato Kotun Shari’a ta Lardi da ke Unguwar Jaki da Kotun Shari’a ta Tudun Alkali sauya salon sauraron karar.Matasan sun […]

Matasan da suka halarcin zaman shari’ar wadanda ake zargi da aikata luwadi a Bauchi sun fusata inda suka nemi yin rajamu ga wadanda ake zargin, lamarin da ya sanya alkalan kotuna biyu da ke shari’ar wato Kotun Shari’a ta Lardi da ke Unguwar Jaki da Kotun Shari’a ta Tudun Alkali sauya salon sauraron karar.
Matasan sun yi ta ruwan duwatsu da kwalabe a kan ginin kotu da motocin gidan yari da nufin sai an ba su mutum bakwai da ake zargi su zartas musu da hukuncin kisa.
Wakilinmu ya ce sai dai jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, kafin su tarwatsa matasan a harabar kotun da ke Unguwar Jaki.
Alkalin Kotun Mai shari’a El-Yakub Aliyu da ya saurari shari’ar mutum bakwai da suka hada da tsohon shugaban makarantar sakandare ta Maina-Maji, Ibrahim Marafa da Shehu Adamu da Yusuf Adamu da Abdulmalik Tanko da Hafiz Abubakar da Usman Sabo, ya nemi a kawo karin shaidu da dalilai masu karfi game da tuhumar da ake yi musu.
Ya ce limamai sun hau mumbari a masallatai sun yi huduba kan illar wannan aiki da kuma mamakin yadda har aka samu kungiya a Jihar Bauchi mai magoya baya 168 tare da samun tallafin Naira miliyan biyar daga kungiyar ’yan luwadi ta Amurka kamar yadda kafafen labarai suka ruwaito.
Ya bukaci ’yan Hisba da lauyan gwamnati su kawo shaidusu, inda ya daga sauraron karar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.
A lokacin da matasan suke ruwan duwatsu da kwalabe wasu jami’an gidan yari biyu sun samu rauni.
A kotun Tudun Alkali inda ake sauraren karar mutum biyu da ake tuhuma da kasancewa cikin kungiyar luwadi, Alkalin Kotun Malam Nuhu Mohammed Dumi ya dage ranar sauraron karar zuwa lokacin da za a samar da ingantaccen tsaron da ya kamata. Kuma ya tura wadanda ake tuhuma zuwa zaman kaso domin hakan zai fi zama alheri gare su saboda yadda batun ke daukar sabon salo domin kare rayuwarsu.