Matasa sun yi fada da ’yan Hisbah a wurin kwacen giya a Kano
Fada ya kaure bayan matasan unguwar Sabon Gari sun nemi hana jami’an Hisbah kwace giya
An ba hamata iska tsakanin jami’an Hukumar Hisbah a jihar Kano da wasu matasa a lokacin da ’yan Hisban suka kai samame a wani wurin sayar da giya da zummar kwacewa.
’Yan Hisbah sun kai samamen ne a wani gidan giya mai suna Ballat Hughes da ke kan Titin Kotu a unguwar Sabon Gari domin kwace giyar amma matasan unguwar suka nemi su hana su.
- Kisan gilla: Sakkwatawa sun ba Buhari wa’adin kwana 14 ya je musu ta’aziyya
- Cutar Zazzabin Lassa ta kashe likitoci 2 a Nasarawa
Ana cikin haka ne fusatattun matasan suka kai wa jami’an hari, lamarin ya rikide zuwa kazamin fada tsakanin bangarorin a gidan gidar wanda mallakin wata mata ce; matasan kuma yi kone-konen tayoyi a kan titi.
Mazauna unguwar sun ce hatsaniyar ta jefa su cikin tashin hankali a yankin a yayin da ’yan daba suka yi amfani da damar wurin fasa kantuna suna satar kayayyaki tare da yi wa mutane masu wucewa kwace.
Daga baya ’yan sanda sun yi nasarar shawo kan lamarin.
A jihar Kano an haramta sha da fataucin giya bisa tsarin Shari’ar Musulunci, amma a Sabon Gari, inda yawancin mazauna yankin ’yan yankin Kudancin Najeriya ne, ba a aiwatar da dokar.
Kakakin ’yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Samaila Dikko ya sa a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma har an kama mutum biyu da ake zargi da laifi.
A cewarsa, ko a kwanakin baya wasu masu otal-otal a jihar sun kai wa Kwamishinan ’Yan Sandan kara kan salon aikin ’yan Hisbah.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan zai ci gaba da tuntubar Hisbah domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar.
Ya kuma bukaci jama’ar Sabon Gari da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin bin doka.
Wakiliyarmu ta nemi tattaunawa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Hisban, Lawan Ibrahim Fagge, amma ya ce ta bari daga baya za a gudanar ta taron ’yan jarida.