Matasa za su yi aiki don ganin Jam’iyyar APC ta karbe mulki daga PDP a zaben 2015 – Dawakin Tofa
Injiniya Mu’azu Magaji Dawakin Tofa shi ne jagoran kungiyar Matasan APC ta APC Youth banguard ya shaida wa Aminiya cewa matasa za su yi aiki domin ganin Jam’iyyar APC ta karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP a zabubbukan 2015 a duk fadin kasar nan: Aminiya: Ga shi kun kafa wata tsangaya ta jam’iyyarku ta APC […]
Injiniya Mu’azu Magaji Dawakin Tofa shi ne jagoran kungiyar Matasan APC ta APC Youth banguard ya shaida wa Aminiya cewa matasa za su yi aiki domin ganin Jam’iyyar APC ta karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP a zabubbukan 2015 a duk fadin kasar nan:
Aminiya: Ga shi kun kafa wata tsangaya ta jam’iyyarku ta APC da kuke kira APC Youth banguard, mene ne manufofinta?
To, yadda muka yi tunanin kafa wani dandali a cikinta domin tafiyar da harkokin matasa. Kamar yadda aka sani, ita siyasa ana yin ta ne domin a samu wani mataki na kama shugabanci wanda zai taimaki al’umma a tsari irin na dimokuradiyya. Sannan idan aka dubi siyasar da ake yi a kasar nan za a ga cewa matasa su ne a sahun gaba wajen juya akalar mafiya yawan bangarori na mulki ko jagoranci, hakan c eta sanya muka kafa wannan tsagi na matasan jam’iyyar APC a kasa baki daya.
Aminiya: Akwai shugaban matasa a kowace jam’iyya, ba ka ganin wannan ofishi zai iya tafiyar da al’amuran matasa?
Dawakin Tofa: Babu shakka akwai shugaban matasa a kowace jam’iyya, amma ai mu ka ji mun ce Youth banguard, wanda dandali ne na matasan jam’iyyarmu ta APC domin ganin matasa ba a bar su a baya ba a harkar siyasa. Sannan shi kansa ofishin shugaban matasa na jam’iyyar yana wakiltar duk wani matashi ne a jam’iyyar, don haka babu wata matsala tsakanin banguard da ofishin jam’iyya a kowace jiha ta kasar nan.
Aminiya: Me kuke so ku cimma a matsayinku na matasan Jam’iyyar APC?
Dawakin Tofa: Babban abin da muka sa a gaba shi ne mu hade kan matasan jam’iyyarmu ya kasance muna magana da murya daya. Sannan za mu yi aiki sosai domin ganin jam’iyyar ta samu nasarar lashe zabubbukan badi (2015) tun daga Shugaban kasa zuwa gwamnoni da ’yan majalisun jihohi cikin yardar Allah. Haka muna da tsari ingantacce na ganin cewa bayan zabe, matasa sun kasance ckin gwamnati sosai domin su ba da gudummawarsu a matsayinsu na kashin bayan ci gaban kowace kasa a duniya.
Aminiya: Kasancewar kungiyarku ta kasa ce, ta yaya kuka kakkafa shugabanci a jihohi 36 da Birnin Tarayya?
Mun kasance cikin aiki babu kasala har sai da muka tabbatar kowace jiha ta samu shugabanni da suke tafiyar da harkokin matasa na APC Youth banguard, kuma alhamdulillahi mun cimma nasara. Sannan duk jihar da ka zagaya za ka ga cewa APC Youth banguard ta kafu domin tunkarar zabubbukan 2015.
Aminiya: Idan muka dawo gida Kano, yaya kungiyarku take ganin cewa APC ce ke jagorancin jihar?
Dawakin Tofa: Babu shakka APC Youth banguard ta kafu sosai a Jihar Kano domin yanzu duk kananan hukumomin jihar 44 muna da ofisoshin kungiyar kuma duk mazabar da ka shiga za ka tarar akwai shugabanci na APC Youth banguard da ke aiki da gaske don ganin Jam’iyyar APC ta mulki kasar nan.
Don haka ina godiya ga matasa kan yadda suka fahimci manufofin wanan tafiya tamu da take da cikakkiyar nasara a siyasar Najeriya da ci gaban dimokuradiyya.Kuma muna alfahari da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso saboda kasancewarsa jagoran Jam’iyyar APC da yadda yake matukar kokari da kwazo don kare martabar dimokuradiyya. Hakika muna jin dadin yadda Gwamnan yake jan ragamar mulkinsa bisa adalci da sanin ya kamata. Ina kara kira ga al’ummar Jihar Kano su fahimci cewa jagoranmu Gwamna Rabi’u Kwankwaso shugaba ne mai hangen nesa idan aka dubi irin ci gaban da ya kawo mana a jihar a kowane fanni na inganta jin dadin rayuwar al’umma.
Aminiya: Mene ne sakonka ga matasan kasar nan musamman ganin yadda suke taka rawa a harkokin siyasa?
Dawakin Tofa: Ina kira ga matasan kasar nan su sani cewa ba su da wata kasa sai Nkjeriya. Don haka wajibi ne su kasance masu aiki da hankali a lokutan zabe da bayan zabe. Kada mu bari ’yan siyasa su yi amfani da mu wajen iza wutar rikice-rikicen siyasa musamman bayan zabe. Matasa a tsaya a gudanar da harkokin siyasa domin kawo wa kasar nan ci gaba mai ma’ana musamman ganin cewa dimokuradiyya ta kafu yanzu a kasar. Kuma ina kara jawo hankalin matasan jam’iyyarmu ta APC su kara jan damarar taimaka wa jam’iyyar ta yadda za ta karbe mulki daga hannun Jam’iyyar PDP don kawo sauyi da shugabanci mai inganci.