Matasa:Kukan kurciya jawabi ne

Mu yi nazari akan rayuwar matasa gami da bada shawarwari don ganin mun zama abin alfahari da kuma amsa sunan mu na manyan gobe. A yau na yi shirin zai waiwayen da Hausawa ke cewa adon tafiya dan hararo rayuwa irin ta matasan baya da sukayi musamman da a wancan lokacin ba kayan more rayuwa […]

Matasa:Kukan kurciya jawabi ne
Matasa:Kukan kurciya jawabi ne

Mu yi nazari akan rayuwar matasa gami da bada shawarwari don ganin mun zama abin alfahari da kuma amsa sunan mu na manyan gobe.

A yau na yi shirin zai waiwayen da Hausawa ke cewa adon tafiya dan hararo rayuwa irin ta matasan baya da sukayi musamman da a wancan lokacin ba kayan more rayuwa kamar su;
wayar hannu da tauraron dan Adam (setelite), internet da sauran su, kuma mu yi mukarana (hadawa) da tasirin su wurin kyautata ko gurbata rayuwar matasanmu na wannan lokaci.
Ga matashi mai karancin shekaru iri na ko sama da haka, in muka duba shekaru talatin baya,
gaskiyar Magana ko biyayya ta sha banban da matasan yau.
Zan tsakuro wasu daga cikin al’adun da matasan wancan zamani ke gudanarwa wanda yanzu suka rikide suka koma kallon kwallo, buga kwallon, kallon sinima, kallon fina-finan batsa da na Turawa da na Indiya kodayake ko a da ana kallon Indiya, wanda shi ma na yanzu ya sha bamban da na wancan zamanin.
Don a wancan lokacin a gaskiya ko da fina-finan Indiya za ka ga ba irin shirmen nan da za ka ga mace da namiji suna rungumar juna, ba kamar yanzu ba.
1-A wancan lokacin, samari da magidanta da an ce an yi sallar isha’i kowa zai fito da abinci a ci, wanda yanzu ba haka abin yake ba.
2-Wasan dandali, wanda maza akwai irin na su mata ma haka, kuma duk a kofar gida, kuma da
an ce lokacin rufe gida ya yi kowa zai shiga gida a kulle, sai kuma Allah ya kaimu gobe. Amma ka hada da matasan mu na yau da ko gidan ba su kwana?
3-Sanya sutura ta kamala, ban mantawa Daraktan A Daidaita Sahu a Kano, Dokta Bala Muhammad, yayin wata lacca da ya yi mana, yake cewa, a da in za su yi tafiya da mahaifin su in suka sanyo kaya zai kale su, ya ce ku koma ku sako kaya’, a nan yana nufin su je su saka babbar riga da wando da hula. Shi kuma yanzu, ya ce in ya umurci ‘ya’yan sa da su saka kaya yana nufin su saka dogayen riguna da wando da hula, shi ne yake tsoron in ‘ya’yansa suka tashi da me za su umurci ‘ya’yan su? Ta kai ga yanzu iyaye in salla ta yi kudi suke dauka su ba ‘ya’yan su wai su je su sayi duk irin kayan da suke so.
4-Tsawata wa yara, a wancan lokacin dan wani shi ne naka, naka kuma na wani, don haka sai ka ga yaro na tsoron ya aikata abu marar kyau gaban na gaba da shi. Yanzu kuwa kowa nasa nasa ne, in ma wani ya yi laifi ka ce za ka doki dan wani, karshe kotu za ta raba ku. An ce kukan kurciya jawabi ne.

Abubuwan da ke halakar da matasa
1-Shaye-shaye,
2-Kallace-kallace,
3-Zaman kashe wando
A yau cikin ikon Allah zan tabo wasu daga cikin manyan sabubba da ke da nasaba da fadawar da yawa daga cikin matasan mu wani mawuyacin hali. Illa ta farko kuma wadda ita ce jagorar duk wata Illa ita ce;
1-Zaman kashe wando;
kila ku yarda da ni in na ce “rashin aikin yi na iya jaza wa matashi shaye-shaye, shaye-shayen kuma shi ne tsanin da za ka taka ya kai ka ga duk wani mummunan aiki”.
Yau a kasar mu mafiya yawan matasan mu ba su aikin komai sai zaman kashe wando, inda ta kai gawasu daga cikin ‘yan siyasar mu suke amfani da su don su zame masu ‘yan bangar siyasa.
Ba lallai ba ne sai gwamnati ta samarwa da daukacin al’ummarta aikin yi ba, amman a ce a kalla mafiya yawanta ya zama suna da hanyar samu, kama daga gwamnatin tarayya zuwa ta jiha zuwa kananan hukumomi, Kamar yadda wasu matakan da na ambata a sama musamman gwamnatin jiha da su samu hanyoyi da za su bunkasa rayuwar matasa, ta hanyar koya masu sana”o’i da ba su da jari, in sun kammala ba su horon, kamar yadda na sani wasu daga cikin jihohin mu suna yi.
Tabbas wasu gwamnatocin duk wata suna raba basussuka ga matasa, haka an samu wasu da suka bude wata masana’anta suna koyar da ‘yan uwa matasa, sai dai inda gizo ke sakar, a gaskiyar magana da yawa daga cikin shirye-shiryen ayyukansu ba su zuwa ga wadanda suka cancanta, sai ka ga an saka siyasa a ciki da sauran su.
A nan zan yi kira ga gwamnati da ta dauki dukkan al’ummar ta a matsayin uwa daya, domin in kana takamar kai ka gyara ’ya’yanka na wani kuma ko oho, to karshe in wadancan da suka lalace sai ka ga sun shafi naka.
A takaice zan dakata akan abin da ya shafi illar rashin aikin yi, kuma kamar yadda na yi kira ba sai gwamnati ba, masu kudin mu da ‘yan kasuwar mu su ma fa dole sai sun taimaka don bai yiwuwa a zura wa gwamnati ido ita kadai duk da ita ce mai babban hakki.
2-Kallace-Kallace;
Ta wadannan kafafe ne matasan mu ke daukar duk wasu bakin dabi’u, kama daga aski, saka wando ko suture da sanya sarka a wuya, sanya ‘yan kunne, sanya katon tabarau da sauran su.
A yanzu wasu iyayen sun dauki wadannan kafafe a matsayin abokan hira, ni kuma na kira su abokan shashanci.
Daga lokacin da matashi ya siffantu da kamanni irin na wasu mutane sannu a hankali sai ka ga dabi’un sa sun rikide sun koma na su.
Wasu malaman tarbiyya sun ce; ko makiyayi ne da ke yawan cudanya da dabbobi to tabbaci hakika zai dauki halayya irin ta wadannan halittu da yake damfare da su kowane lokaci, ballantana ace wasu jinsuna.
Zan yi kira ga iyaye wadanda kai tsaye suke da hakkin kula da da walwalar ’ya’yansu, da kada su sakar masu tashoshi, musamman na batsa da kade-kade da kallace-kallacen fina-finai kama da ga na Hausa ko Turanci ko Amurkawa da sauran su.
Haka kar su bar su da wayoyin hannu, kamar yadda na sha fada sai ka ga yarinya ‘yar shekara 12 tana rike manyan wayoyin da hankali bai daukar irin ta’asar da sukan iya janyowa.
Hausawa sun ce “gyara kayan ka……”
3-Shaye-shaye;
Annabi SAW ya ce “duk abin da ke sa maye giya ne, kuma kowace giya haramun ce”
Kamar yadda na ambata a sama, ita ba rna matakai gare ta, idan aka rasa aikin yi ga mafiya yawan matasan mu, sai su buge da kallace-kallace, daga nan sai aron al’adu sai shaye-shaye, an ce daga inda turwa tayi fuka-fuki to lalacewar ta ya zo, to haka yake ga matashin da ya riki kayan maye, wata rana sai ka ji shi yana dauke-dauken abin da bai aje ba.
Anan fagen ma zan yi kira ga hukuma wanda hakkin tane kula da kare hankulan al’ummar ta, kuma akwai wasu gwamnatocin da ke kamawa da kona kayan da suka kama wanda abu ne mai kyau.
Allah ya shiryar da mu da zuri’ar da ya ba mu, ya gafarta mana kura-kuran mu kuma yasa mu cika da imani.

Sanusi Hashim Abban Sultana
Daga jihar katsina 08065507271.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno