Matasan Abiya sun caccaki Janar Ihejirika kan taimaka wa murdiyar zabe

Matasan Jihar Abiya da suka fito daga gundumar mazabar Arewa, sun caccaki tsohon Hafsan hafsoshin sojan kasar nan, Janar Azubuike Ihejirika mai ritaya kan yadda ya goyi bayan murdiyar zabe a shekarar 2011. Sannan sun soki lamirin Gwamna T. A. Orji kan rashin tabuka abin a zo, a gani.Wannan taron dai an gudanar da shi […]

Matasan Abiya sun caccaki Janar Ihejirika kan taimaka wa murdiyar zabe
Matasan Abiya sun caccaki Janar Ihejirika kan taimaka wa murdiyar zabe

Matasan Jihar Abiya da suka fito daga gundumar mazabar Arewa, sun caccaki tsohon Hafsan hafsoshin sojan kasar nan, Janar Azubuike Ihejirika mai ritaya kan yadda ya goyi bayan murdiyar zabe a shekarar 2011. Sannan sun soki lamirin Gwamna T. A. Orji kan rashin tabuka abin a zo, a gani.
Wannan taron dai an gudanar da shi ne a Arochukwu da ke Jihar Abiya, inda aka tattauna kan makomar jihar. Taron ya samu halartar masu sana’o’in hannu da dalibai da kwararru a fannoni daban-daban, wadanda suka bukaci tsohon Hafsan hafsoshin sojan kasar nan, Janar Azubuike Ihejirika da ya fito bainar jama’a, ya roki gafara kan yadda ya mara wa murdiyar zabe baya, a zaben shekarar 2011.
Matasan sun bayyana yadda Iherjirika ya hada kai da sojojinsa suka bai wa masu kada kuri’a tsoro, ta hanyar juya alkaluma har Gwamna T.a. Orji da Sanata Uche (daga mazabar Abiya ta Arewa) suka lashe zaben.
Mai Magana da yawun kungiyar matasan, Mazi Ifeanyi Kelechi, a hirar da ya yi da manema labarai ta wayar tarho, ya bayyana cewa: “Mun yanke cewa, mu yi taro a matsayinmu na manyan gobe don tattaunawa kan makomar siyasar Abiya. Manufarmu it ace jajircewar rashin jin tsoron duk wata barazana, sannan mu daura yaki da masu murdiyya a zabuka masu kartowa. Abin da ya faru a zaben da ya wuce ba zai sake aukuwa ba. Za mu kona duk wanda ya juya zaben gaskiya. Makomar mu na nan a kuri’unmu, don haka dole mu kare kuri’unmu. Mun sha wuya a hannun miyagun ’yan siyasa masu son kansu, wadanda ke tursasa jama’a don su shugabance su ko ta halin kaka.”
“Iherijika da kansa ya jagoranci yin barazana ga al’umma, inda ya sa aka tsare daya daga cikin manyan shugabanninmu, wato tsohon Gwamna Orji Kalu a gidansa, ta hanyar amfani motocin yaki hudu, alamarin da ya haifar da tawaya, ba wai ga ’yan takara kawai ba, har ma da daukacin masu kada kuri’a,” inji shi.