Matasan Badinawa Kwankwasiyya na son Kwankwaso ya yi takarar shugaban kasa
Shugaban matasan Arewa na jam’iyyar APC (Badinawa/Kwankwasiyya) a Jihar Oyo, Malam Hamisu Sabi’u Nahannu ya ce a matsayinsu na matasa sun hango cewa, Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne ya cancanci zama dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwar APC a zaben shekara ta 2015. “Irin sababbin ayyukan ci gaban Jihar Kano da gwamnan yake […]

Shugaban matasan Arewa na jam’iyyar APC (Badinawa/Kwankwasiyya) a Jihar Oyo, Malam Hamisu Sabi’u Nahannu ya ce a matsayinsu na matasa sun hango cewa, Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne ya cancanci zama dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwar APC a zaben shekara ta 2015.
“Irin sababbin ayyukan ci gaban Jihar Kano da gwamnan yake yi yanzu haka, a ko’ina a cikin jihar da samar da guraben ayyuka ga matasa da sauran masu neman ayyukan yi da bayar da tallafin rancen kudade ga kungiyoyin ’yan kasuwa da kuma batun ilmi, wanda dalibai ’yan asalin Jihar Kano suke cin moriya a ciki da wajen kasa, suna daga cikin dalilanmu da muke so ya fito domin neman takarar shugaban kasa a shekara ta 2015 domin bauta wa jama’a”. Inji shi.
Malam Hamisu Sabi’u yana fadin haka ne cikin hirarsu da wakilinmu a Ibadan, inda kuma ya ce, “Ya kamata Gwamna Kwankwaso ya ci gaba da ayyukan da yake yi wa jama’a ba tare da sauraron masu hamayya, musamman magoya bayan tsohon Gwamna Shekarau da suke neman dakile ayyukan ci gaban jama’a da suka kasa yi a tsawon shekaru 8 da suka yi suna mulkin jihar ba. Bai kamata wadannan mutane su kafa kahon zuka ga Gwamna Kwankwaso ba. Idan ya yi abun alheri a yaba masa, idan kuma ya yi kuskure ne, ku sanya shi a gaba domin yin gyara, amma bai dace ana cusa mana mummunar gaba a tsakanin matasa da suke kaiwa ga fadace-fadace har da kashe-kashen rayuka a tsakaninsu ba. A matsayinku na iyayenmu, ya kamata ku zo ku sanya mu a kan harsashin da za mu ci moriyarsa a nan gaba, amma ba jefa mu ga halaka ba.”
Shugaban a Jihar Oyo za su fara shiga manyan garuruwan da mutanenmu suke zaune da iyalinsu suna gudanar da harkokin kasuwancinsu domin wayar da kai a game da goyon bayansu ga nufin matasan a shekara ta 2015, don jefa wa Gwamna Kwankwaso kuri’unsu idan ya samu zama dan takarar shugaban kasa. Idan kuwa Allah (TWT) bai kai shi ga wannan matsayi ba to, su fito su goyi bayan alkiblar da ya dosa domin yin adalci da taimakon jama’a.