Matasan da Buhari ya kira malalata ne suka zabe shi- Sanata Ben Murray Bruce

  Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Ben Murray Bruce ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya manta yadda matasan Najeriya da yake kira da malalata suka tsaya cikin rana mai tsananin zafi suka zabe shi.   “Maimakon Buhari ya bincika ya gano dalilin da ya sad a yawa daga cikin ‘yan Najeriya suke fita […]

Matasan da Buhari ya kira malalata ne suka zabe shi- Sanata Ben Murray Bruce

 

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Ben Murray Bruce ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya manta yadda matasan Najeriya da yake kira da malalata suka tsaya cikin rana mai tsananin zafi suka zabe shi.

 

“Maimakon Buhari ya bincika ya gano dalilin da ya sad a yawa daga cikin ‘yan Najeriya suke fita kasashen waje kamar su Kanada domin aiki, Shugaban Buhari sai yake kiransu da malalata.

“Abin ban dariya a nan shi ne yadda wadannan matasan suka tsaya cikin tsananin rana na tsawon lokaci domin su zaba mutumin da yi alkawarin kawo canji, amma sai ya bige da kawo sarka.”

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram