Matasan darikar kadiriyya Nasiriya sun nemi hukuma da malamai su kawo karshen cin zarafin Annabi a kasar nan
Matasa mabiya darikar kadiriyya Nasiriya a Jihar Sakkwato sun nemi hukumomin Najeriya da malaman addinin Musulunci da ke kasar nan su yi hobbasa don kawo karshen cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da wasu zindikai ke yi lokaci -lokaci. Shugaban kungiyar Matasan kadiriyya Nasiriyya ta Jihar Sakkwato Malam Mansur Hallaj ne ya yi wannan […]
Matasa mabiya darikar kadiriyya Nasiriya a Jihar Sakkwato sun nemi hukumomin Najeriya da malaman addinin Musulunci da ke kasar nan su yi hobbasa don kawo karshen cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da wasu zindikai ke yi lokaci -lokaci.
Shugaban kungiyar Matasan kadiriyya Nasiriyya ta Jihar Sakkwato Malam Mansur Hallaj ne ya yi wannan kira a ranar Talatar da ta gabata, yayin zantawarsa da Aminiya a Sakkwato.
Shugaban ya ce “kungiyarsu tana jin takaici kuma tana yin Allah wadai da zindikai masu kokarin kawo fitina a kasa da sunan darikar Tijjaniya wadda mafi yawan malamansu ba su tafi a kan wannan hanya ta zindikanci ba, domin Annabi Muhammad (SAW) yana da girma a wurinsu, kuma suna kare martabarsa a ko’ina cikin karatunsu da ayyukkansu.”
Hallaj ya kara da cewa “Abdul Inyas ya ba mu mamaki tun daga sunansa da ya saba wa shari’a har zuwa kalamansa na cin zarafi ga Annabi (SAW) domin shi kansa Nyass a littattafansa yana kiran kansa da Hadimun Nabiyyi wato mai yi wa Annabi hidima ko baransa ko neman shiga a wurinsa, to yaya bayan haka wasu su zo suna wuce gona da iri da sunan yabonsa wanda haramun ne a Musulunci.”
Malam Mansur ya kara da cewa, “Ya kamata malamai su rika jawo hankalin muridansu su kauce wa fadawa cikin hali ko kalamai na kafirci da ridda da sunan addini, wannan yanayi da ake ciki ya zama wajibi ga malaman kasar nan su fito su yi wa’azin yakar ’yan hakika wato zindikai da hujja don nesantar da mutane hadarin walakanta Annabi (SAW), su kuma hukumomi ko gwamnati dole ne su yi iyakar kokarinsu don kawar da wadannan mutane daga cikin al’umma saboda hakkinsu ne su kare mutunci da rayukan mutane da addininsu.”
Hallaj ya ce “Mutanen nan ba wannan ne karon farko da suke fadin irin wadannan miyagun kalamai ba, amma an kyale su don haka suka kara furta wannan a gaban jama’a wurin Mauludin Inyas a Kano, in ba a taka musu birki ba, wannan batacin zai wuce haka da sunan addini, ba za mu lamunci wannan ba, ko don rudanin da ake samu a Sakkwato duk lokacin da irin wadannan kalamai suka taso. Malamai ko a wace darika ko fahimta suke, to, su ji tsoron Allah da kiyaye martabar Annabi Muhammad (SAW) saboda tserar da al’umma daga fitina.”