Matasan Filato 280 za su amfana da tallafin Babban Bankin Najeriya
Hukumar Bunkasa da Raya Bankuna Karkara ta Jihar Filato (PLASMEDA) ta bayyana cewa ta yi hadin gwiwa da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen horar da matasan jihar 280, inda zuwa yanzu aka tantance su kafin su kai ga amfana da wani kaso daga cikin Naira biliyan 220 da ke karkashin kulawar Bankin Sterling da Bankin […]

Hukumar Bunkasa da Raya Bankuna Karkara ta Jihar Filato (PLASMEDA) ta bayyana cewa ta yi hadin gwiwa da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen horar da matasan jihar 280, inda zuwa yanzu aka tantance su kafin su kai ga amfana da wani kaso daga cikin Naira biliyan 220 da ke karkashin kulawar Bankin Sterling da Bankin CBN ya ware don tallafa wa masu kananan sana’o‘I da masana’antu.
Darakta Janar na hukumar, Mista Haggai H Gutap wanda Daraktan, Hukumar Kula da kanana da Matsakaitan Masana’antu (MSME), Mista Joseph Bewa ya wakilta ne ya bayyana hakan, yayin bikin bude taron horar da matasan Jihar Filato 3, 230 da nakasassu 38 kan kananan sana’o’i da kasuwanci, wanda ya gudana a Cibiyar Matasa ta Azi Nyako da ke Jos a ranar Asabar din da ta gabata.
Mista Gutap ya bayyana cewa wadannan matasa 280 kowannensu zai iya samu adadin Naira miliyan 3 matukar kasafin abin da zai yi ya kai adadin hakan.
Ya ce, Bayan wani nazari da bincike da muka yi mun gano kananan sana’o’i da masana’antu suna mutawa a Jihar Filato, inda abubuwa suke ci gaba da tabarbarewa. kananan masana’antun suna mutuwa ne sakamakon rashin sanin makamar kasuwanci, rashin isasshen jari, rashin kasuwa da sauransu.
Ya bayyana cewa bayan nazarin da suka yi ne ta sanya hukumarsu ta tashi tsaye wajen ganin ta shawo kan matsalolin ta hanyar horar da matasa da ba su dabarun kasuwanci da kuma taimaka musu da jari don su tsaya da kafafunsu har ta kai ga sun iya daukar wadansu aiki.
Ya ce, “A yanzu gwamnati ta kai wani mataki na cimma yarjejeniya da Bankin Bunkasa Masana’antu (BOI) wajen samo wa matasa bashin da zai taimaka musu don bunkasa kasuwancinsu da kuma sana’o’insu, amma ba kowa za a ba ba, sai wanda ya ya cika dukkan ka’idoji da sharadodin da aka gindaya