Matasan Gwallaga sun kafa kwamitin gyaran tarbiyya

Tun lokacin da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rulwanu Suleiman Adamu ya ba da umarnin a kirkiro wani kwamiti da zai rika sa-ido sosai wajen gyaran tarbiyyar matasa da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi a cikin unguwani, matasan unguwar Gwallaga da ke garin Bauchi suka kafa wani kwamiti na gyaran tarbiyya. Da yake zantawa da […]

Matasan Gwallaga sun kafa kwamitin gyaran tarbiyya
Matasan Gwallaga sun kafa kwamitin gyaran tarbiyya

Tun lokacin da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rulwanu Suleiman Adamu ya ba da umarnin a kirkiro wani kwamiti da zai rika sa-ido sosai wajen gyaran tarbiyyar matasa da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi a cikin unguwani, matasan unguwar Gwallaga da ke garin Bauchi suka kafa wani kwamiti na gyaran tarbiyya.

Da yake zantawa da wakilin Aminiya kan yadda kwamitin take gudanar da ayyukansa shugaban kwamitin Alhaji Ibrahim Ahmed ya ce an samu gagarumar nasara sakamakon kafa kwamitin, inda da yawa daga cikin matasan da suke shan miyagun kwayoyi suka tuba.
Ya ce akwai matasa sama da 400 da suka tuba daga sace-sace da shan miyagun kwayoyi, kuma za su ci gaba da wayar da kan matasa kan illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi musamman a wannan lokaci na mulkin siyasa.