Matasan Ikorodu sun yaba farmakin da sojoji suka kai wa masu fasa bututu
Matasa a al’ummar Ikorodu dake Jihar Legas, sunnuna gamsuwarsu kan irin kokarin da rundunar sojan Najeriya da na ruwa ke yi wajen shawo kanaikata miyagun laifuka a yankin.Matasan sun bayyana cewa, a wani farmaki da jami’an tsaron sukakai wa masu fasa bututun man fetur, ya sanya har mutum 50 sun shiga hannu, inda aka kwace […]
Matasa a al’ummar Ikorodu dake Jihar Legas, sunnuna gamsuwarsu kan irin kokarin da rundunar sojan Najeriya da na ruwa ke yi wajen shawo kanaikata miyagun laifuka a yankin.
Matasan sun bayyana cewa, a wani farmaki da jami’an tsaron sukakai wa masu fasa bututun man fetur, ya sanya har mutum 50 sun shiga hannu, inda aka kwace jarkoki fiye da dubu cike man fetur din sata.
A wata sanarwa da matasan suka bayar, sun tabbatar da kokarin da jami’an tsaron farin kaya na “Cibil Defence” suka yi, har akazarge su da wuce iyaka.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Moshood Adebayo, ya koka kan yadda aka yi wa Ikorodu lakabi da sansanin masu fasa bututu, amma wannan farmakin da sojoji suka kai ya fito da gaskiyar lamari, ta yadda za a fahimci cewa masu aikata laifuka ba lallai mazaunan yankin ba ne.
“Muna sanar da cewa fasa buttu ba shi da alaka da mutanen da muke zaune da su a wannan yanki, domin muna aiki tare da gwamnati wajen ganin an bayar da kariya ga dukiyar al’umma,” kamar yadda yake kunshe a sanarwar.