Matasan Jigawa sun yi zanga-zanga kan kama ’ya’yan Gwamna Lamido
daruruwan matasa da suka fito daga kananan hukumomin jihar 27 sun yi zanga-zanga daga hedikwatar Jam’iyyar PDP zuwa Majalisar Dokokin Jihar suna rera wakokin kin jinin Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Allah wadai da Gwamnatin Tarayya kan kame ’ya’yan Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido.Matasan sun rika rera wakokin dole a samu canji a shekarar 2015, […]

daruruwan matasa da suka fito daga kananan hukumomin jihar 27 sun yi zanga-zanga daga hedikwatar Jam’iyyar PDP zuwa Majalisar Dokokin Jihar suna rera wakokin kin jinin Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Allah wadai da Gwamnatin Tarayya kan kame ’ya’yan Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido.
Matasan sun rika rera wakokin dole a samu canji a shekarar 2015, kuma dole ne Bamanga Tukur ya sauka daga shugabancin Jam’iyyar PDP.
Matasan wasu a kan kekuna, wasu a babura da motoci, wasu a kasa, da suka samu tarbar daga Shugaban Majalisar Jihar da wasu kusoshinsa, suna nuna alhininsu kan kame ’ya’yan Gwamnan Jihar, wato Hakimin Bamaina, Alhaji Mustapha Sule Lamido da dan uwansa Aminu Sule Lamido bisa zargin da hannunsu a wata badakalar ta Naira biliyan 10.
Matasan a karkashin jagorancin Kwamared Musa Gambo Guri, sun ce muddin Gwamnatin Tarayya ba ta sako ’ya’yan Gwamnan ba za su yi wani gangami da zai tada hankalinta. “Dole a saki ’ya’yan Gwamnan a sakarmusu mara, mene ne hadinsu da siyasa da za a kama su?,” inji Gambo Guri.
Matasan sun ce Shugaba Jonathan bai yi wa jama’ar Jigawa adalci ba in har ya ce gwamnatin jihar ba ta kashe kudaden da take samu daga asusun tarayya ta hanyar da ta kamata ba.
“Kada Shugaba Jonathan ya manta ya yaba wa Lamido lokacin da ya bude Dandalin Yakubu Gowon da gwamnatin jihar ta gina ga masu yi wa kasa hidima a matsayin masauki a kan Naira miliyan 11 sabanin wasu jihohi da aka gina irinsa a kan Naira biliyan biyu,” inji jagoran.
Da yake mayar da jawabi Shugaban Majalisar Alhaji Adamu Ahmed Sarawa ya ce gwamnati da majalisar za su yi bakin kokarinsu don mara wa matasa su kai ga nasara. “Koda yake wannan fadan manya ne da bai sauko kasa ba, a duk lokacin da fadan ya sauko kasa babu makawa a shirye suke su fada ciki domin ba za su sanya ido ana cin mutuncin shugabansu su kyale ba,” inji shi.
Adamu Sarawa ya nuna takaici a kan yadda ake wa gwamnati da shugabannin jihar bi-ta-da-kulli ta barazana da EFCC da ICPC, “wannan barazana da musgunawa ba za su sa mu kauce wa akidarmu ba, domin kawai mun ce sai an yi gaskiya sai a ce wai ba ma tare da Gwamnatin Tarayya in dai a kan gaskiya ne babu dalilin da zai sa a ce mun karkata akalarmu zuwa tafarkin rashin gaskiya,” inji shi.