Matasan Kano sun kone A Daidaita Sahu kan zargin kwacen waya
Wasu fusatattun matasa a unguwar Kabuga da ke Kano sun kone wani babur mai kafa uku, bisa zargin na masu kwacen waya ne.
Matasa sun kone wani babur mai kafa uku, wanda aka fi da A Daidaita Sahu, bisa zargin na masu kwacen waya ne a unguwar Kabuga da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano .
Fusatattun matasan sun dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da wasu al’ummar jihar ke kiraye-kirayen a kafofin sada zumunta kan daukar mataki kan masu kwacen waya, saboda a yadda bata-garin suka addabi jama’ar jihar.
Kano na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi kaurin suna wajen ayyukan masu kwacen waya ta hanyar amfani da makami.
Ko a makon jiya, sai da wasu masu kwacen waya suka caka wa wani matashi wuka suka kashe shi a Hauren Legal, kusa da Kwalejin Nazarin Aikin Shari’a na Aminu Kano.
- Ba zan daina rusau da korar ma’aikata ba, har sai na bar mulki —El-Rufai
- Mutane da dama sun kone a hatsarin tankar mai a hanyar Abuja
Aminiya ta ruwaito yadda masu kwacen waya suka gota kashi bayan wata mata, suka kwace mata waya a unguwar Nassarawa da ke jihar.
A makon jiya ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar cewa daga yanzu za ta rika gurfanar da masu kwacen waya a gaban kotu ne a matsayin ‘yan fashi da makami.
Masu kwacen waya sun yi ajalin mutane da dama, baya ga wadanda suka jikkata ko suka raba da dukiyoyinsu.