Matasan Katsina sun kaurace wa zanga-zanga

Kungiyoyin ’yan kasuwa ma sun kauracenwa zanga-zangar, saboda a cewarsu, dukiyarsu ake barnatawa a lokacin zanga-zanga

Matasan Katsina sun kaurace wa zanga-zanga

Wakilin kungiyoyin matasan Katsina, Aliyu Idris Zakari, ya shelanta cewa matasan jihar ba za su shiga wannan zanga-zangar dake tafe kan tsadar rayuwa a Najeriya ba.

Aliyu Idris Zakari ya ce sun yanke shawarar kaurace wa zanga-zangar ce bisa lura da suka yi da irin abubuwan da suka faru a wasu kasashe irin suLibiya da abin da ke faruwa a Kenya a halin yanzu.

Bisa haka ne suka nesanta kansu daga shiga cikin wannan zanga-zanga duk da cewa sun san sauran takwarorinsu a kasar da za su shiga.

Su ma ’yan kasuwar jihar Katsina, sun kaurace wa zanga-zangar, saboda a cewarsu, a karshe a kansu abin ke karewa, inda ake  barnata masu dukiya.

’Yan kasuwar sun nemi gwamnati da ta nemo sauran kungiyoyi don zama a samo hanyoyin da ya dace don samun zaman lafiya da kawo saukin rayuwa a jihar da ma kasa baki daya.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta