Matasan Sabuwar Gandu sun kashe barawon da ke kashe musu amare

A ranar Alhamis din makon jiya ne matasan Unguwar Sabuwar Gandu da ke Kano suka yi kwanton bauna ga barayin da ke shiga gidajen amaren unguwar suna kashe su tare da yi musu sata, inda suka kama wani saurayi su ka kashe shi.Lamarin ya faru ne da rana inda matashin mai suna Nafi’u Yakubu ya […]

Matasan Sabuwar Gandu sun kashe barawon da ke kashe musu amare
Matasan Sabuwar Gandu sun kashe barawon da ke kashe musu amare

A ranar Alhamis din makon jiya ne matasan Unguwar Sabuwar Gandu da ke Kano suka yi kwanton bauna ga barayin da ke shiga gidajen amaren unguwar suna kashe su tare da yi musu sata, inda suka kama wani saurayi su ka kashe shi.
Lamarin ya faru ne da rana inda matashin mai suna Nafi’u Yakubu ya shiga gidan wata amarya mai wata shida da aure, inda ya shake mata wuya. Da ya fahimci cewa ta mutu sai ya yasar da ita a gefen daki ya shiga cikin dakin ya dauki wasu kayayyakinta da suka hada da sababbin atamfofi da kudinsu ya kai Niara dubu 28.
Sai dai Nafi’u bai san cewa matasan unguwar sun yi masa kwanton bauna ba, yana fitowa daga gidan suka yi kansa da duka har sai da ya daina numfashi. Daga nan ne ’yan sanda suka dauke shi zuwa Asibitin Murtala daga bisani ya ce ga garinku nan.
Wani wanda abin ya faru akan idonsa da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa wasu leburori da ke gini a kusa da gidan ne suka ga fitar barawon daga gidan amaryar inda suka yi hanzarin kama shi tare da sanar da jama’ar unguwar, inda su kuma suka fada masa da duka da sara.   
Ita ma amaryar da balahirar ta faru a kanta mai suna  Zuwaira Adamu ta shaida wa Aminiya cewa, “Bayan na fito daga wanka ina zaune ina sa kaya, sai na ji kamar motsin mutum a gidan, sai na fito domin na ga me ke faruwa.  Kawai sai na ji an shake min wuya, aka yi cikin daki da ni aka kwantar. Ba kokarin da ban yi na kwaci kaina daga hannunsa ba, amma na kasa har na suma.”
Ta ce “Ban tashi farfadowa ba sai bayan lokacin da aka bugo kofar gidan, inda aka kai ni Asibitin Murtala, kafin a sallame ni daga baya.”  
Aminiya ta tattauna da mutanen unguwar don jin ta bakinsu game da matakin da za su dauka a kan wanann lamari, inda Malam Shitu Magaji ya bayyana cewa a yanzu haka sun yanke shawarar daukar ’yan sintiri na musamman wadanda za su rika yi musu gadi a unguwar.
Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki ta hanyar samar da karin ofisoshin ‘yan sanda a wannan unguwa tasu ta Sabuwar Gandu tare da wadata su da isassun kayan aiki.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce bayan lamarin ya faru ’yan sanda sun kai amaryar da barawon Asibitin Murtala, inda daga bisani wanda ake zargin ya cika. “Sai dai kafin wanda ake zargin ya cika ya amsa laifinsa, inda ya ce yana daga cikin wadanda suka kashe amaryar Daraktan Labarai a Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Kano bayan kwana goma da yin bikinsu. Haka kuma mun gano cewa Nafi’u dan asalin garin Zariya ne a Jihar Kaduna,” inji shi. Majiya ya ce yanzu haka ana ci gaba da bincike don gano sauran mutanen da ke da hannu a kashe-kashen amaren da aka yi a unguwar ta Sabuwar Gandu.   
Idan za a iya tunawa wannan shi ne karo na uku da barayi ke shiga gidajen amare a Unguwar Sabuwar Gandu suna kashe su tare da kwashe musu dukiya.