Matasan Sakkwatawa sun gana da sardaunan matasan Jihar Sakkwato
Ranar Lahadi wadansu shugabannin matasan Sakkwatawa a Jihar Legas suka gana da Sardaunan matasan Jihar Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele, inda suka tattauna dangane da irin gudunmawar da za su bayar domin samun nasarar shirin samar da ayyuka ga matasa da Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako yake yi a Jihar Sakkwato.Da yake yi wa ’yan jarida […]

Ranar Lahadi wadansu shugabannin matasan Sakkwatawa a Jihar Legas suka gana da Sardaunan matasan Jihar Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele, inda suka tattauna dangane da irin gudunmawar da za su bayar domin samun nasarar shirin samar da ayyuka ga matasa da Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako yake yi a Jihar Sakkwato.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani jim kadan bayan tattaunawa, Sardaunnan matasa, Alhaji Mujitaba Isa Helele, ya jinjina wa Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako dangane da bullo da shirin samar da ayyuka ga matasa da bude cibiyoyin koyon sana’o’i da ayyukan yi, wanda dubban matasa, maza da mata, suke cin moriyarsa yanzu. Ya kuma nemi gwamnatin ta bullo da dabarun da za su tabbatar da dorewar shirin ya kasance na dindindin a jihar.
Ya ce, “Bayan an sami hakan, ya dace kuma gwamnati ta tabbatar da ganin tallafin kayan aiki suna wadata kuma suna isa hannun matasan, wadanda suka koyi ayyuka da sana’o’in, kai-tsaye, ba tare da barinsu salun alun ba. Kuma ya kamata a bullo da sabon salo da zai janyo matasa su kusanci gwamnati ba a rika yin nesa da su ba. Kusantar da matasa ga gwamnati yana da muhimmanci domin yana karfafa musu guiwar rungumar kowane kyakkyawan tsari, musamman ma shirin samar da ayyuka da sana’o’i, amma rashin janyo su a jika yana haifar da karuwar miyagun dabi’u a tsakaninsu, alhali su ne manyan gobe”.
Sardaunan ya ba da misali da wani bincike da suka gudanar a Jihar Sakkwato, inda suka gano cewa, wasu matasan da gwamnati ta dauki dawainiyar horar da su tare raba musu kayan aiki kyauta, sun rika cefanar da kayan a wulakance suna komawa cikin halin ni-’yasu da bata sunan gwamnati. Saboda haka ya bukaci dukkan wanda ya samu irin wannan tallafi, ya daure ya yi amfani da shi tsakani da Allah, kada ya rinka yi wa shirin rikon sakainar kashi.
Ya ce ziyarar da ya kai zuwa wasu cibiyoyin koyar da matasa a jihohin Kudu maso Yamma ta ba shi sha’awa, musamman saboda irin zage damtse da gwamnatocin suka yi wajen dorewar shirin da kuma irin amsa kiran matasan da suka ci moriyar shirin suka yi, wajen kafa kungiyoyin gama-kai domin ci gaba da samun tallafi daga gwamnati wajen bunkasa sana’o’insu. “In Allah Ya yarda zan yi kokarin ganin mun koyi irin wannan a Jihar Sakkwato, domin kasashen duniya daban-daban da suka ci gaba, su ma da rarrafe suka tashi. Za mu yi hobbasa wajen wayar da kan matasa domin cimma buri”. Inji shi.
Daga nan sai ya nemi matasa, musamman a Jihar Sakkwato, su yi taka-tsantsan wajen jefa kansu cikin rikicin siyasa, amma su yi kyakkyawar natsuwa wajen lura da mutanen kirki masu kishin al’umma da ci gabansu da za su zaba a mazabunsu domin yin adalci.
A karshe ya jinjina wa Mai Alfarma Sultan na Sakkwato, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar saboda matakan da yake dauka wajen hada kawunan musulmi a Najeriya. Ya roki Allah Ya yi wa Sultan jagorancin ci gaba da wannan aiki.
Tun farko a jawabinsa, daya daga cikin shugabannin Sakkwatawan, Alhaji Murtala Abubakar (Walima) ya nemi Sardaunan matasan ya kai irin wannan ziyara sauran jihohin Kudu, lamarin da zai karfafa wa Sakkwatawa mazauna wannan sashe kwarin guiwar tashi tsaye wajen rungumar sana’o’i da ayyukansu. Yin hakan kuma zai rage yawan kame-kamen da jami’an tsaro suke yi musu ba takamaiman dalili.