Matashi mai fataucin mutane ya shiga hannu a Katsina
Hukumar shigi da fici a Jihar Katsina ta kama wani matashi bisa zargin jagorantar fataucin mutane zuwa kasashe ketare.An kama matashin ne tare da mutum tara da ya yi kokarin tsallakawa da su ta kan iyakar Kongolam ta karamar Hukumar Mai’aduwa a kan hanyarsa ta zuwa Jamhuriyyar Nijar don ratsawa ta cikin saharar Agades zuwa […]

Hukumar shigi da fici a Jihar Katsina ta kama wani matashi bisa zargin jagorantar fataucin mutane zuwa kasashe ketare.
An kama matashin ne tare da mutum tara da ya yi kokarin tsallakawa da su ta kan iyakar Kongolam ta karamar Hukumar Mai’aduwa a kan hanyarsa ta zuwa Jamhuriyyar Nijar don ratsawa ta cikin saharar Agades zuwa Libya don shiga Turai.
Kwantarolan hukumar a Jihar Katsina, Mista Emmanuel N. Ogbumou ya shaida wa manema labarai haka a yayin da yake gabatar da mutum 10, maza tara da mace daya da aka kama, inda ya ce, hukumarsa a shirye take don ganin ta hana wannan muguwar sana’a da ta zamo ruwan dare.
“Fataucin mutane na daga cikin ayyukan tauye hakkin dan Adam ne da ke kokarin mamaye duniya, kuma domin shawo kan matsalar ce ya sa gwamnatin Najeriya hada gwiwa da kasar Italiya da wasu kasashen Turai don ganin an kawar da wannan sana’a ta bautar da mutane.
Mutum tara daga cikin 10 da aka kama duk sun fito ne daga Jihar Edo, biyar daga cikinsu har da madugun tafiyar mai suna Olumese Barnabas mai shekara 28 da wata mai suna Blessing Emma mai shekara 23 sun fito ne daga karamar Hukumar Ishan ta Arewa maso Gabas. Sai mutum uku daga karamar Hukumar Uromi da mutun daya daga Ishan ta Gabas, dukkansu daga Jihar Edo. Sai kuma Ifeanyi Onyeneke mai shekara 25 daga karamar Hukumar Awikasu ta Jihar Imo.
Kwantarollan ya ce, wannan shi ne kamu na uku a cikin wannan shekara, inda aka kama mutum 24, inda aka tura su ga hukumar yaki da fataucin mutane da ke Kano.
Ya ce Barnabas sun yi kokarin amfani da tsofaffin fasfuna don gudanar da wannan muguwar niyya tasu.
Matasan sun ce, sun dauki wannan mataki ne domin neman samun saukin kuncin rayuwa da suke fuskanta a kasar nan.