Matashi mai shekaru 19 ya yi wa ’yar shekara 25 fyade
Kotu ta ki amincewa da bukatar bayar da belin wanda ake zargi da zakke wa mai shekara 25 da karfin tsiya
Wata kotun majistare da ke Ibadan, ta tsare wani matashi mai shekaru 19 kan laifin yi wa wata mai shekaru 25 fyade a gidan kaso.
Dan sanda mai gabatar da kara, Philip Amusan, ya fada wa kotun cewa a ranar 18 ga Satumba ne wanda ake zargin ya auka wa matashiyar da karfin tsiya, ba tare da amincewarta ba.
- Mahara Sun Kashe Mutum 1 Sun Sace Wasu 3 A Zariya
- Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 5.9 sakamakon cutar daji a 2019 —Rahoto
Laifin, a cewarsa ya saba wa sashe na 357, da na 358 na Kundin Manyan Laifukan Jihar Oyo na shekarar 2000.
Alkalin kotun, O.A Akande ta ki amincewa da bukatar ba da belin matashin, sannan ta umarci ’yan sanda su mayar da fayil ɗin karar ga Daraktan Gabatar da Kararrakin Jama’a (DPP) don shawara.
Daga nan ne ta dage shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, 2022.