Matashi mai tsananin son aure ya tallata kansa a allunan talla

Tallan dai na ci masa makudan kudade.

Matashi mai tsananin son aure ya tallata kansa a allunan talla

Daya daga cikin allunan tallar da Malik Mohammed ya saka a Birmingham

Wani matashi da ya ya gaji da zaman tuzuranci, kuma yake tsananin son aure da aka bayyana sunansa da Mohammed Malik, ya sanya hotunansa a wasu manyan allunan talla a Birmingham da ke kasar Birtaniya yana neman matar aure, lamarin da ya lakume masa dubban dalolin daukar nauyin tallar.

Daya daga cikin allunan tallar an ce na kusa da yankin A34 kusa da Unguwar Perry Barr Greyhound Track a Birmingham ta Birtaniya.

A daya daga cikin allunan tallace-tallace mai tsawon kafa 20 wanda wani ya wallafa a shafinsa na Instagram da adireshin @dailystar, an ga matashin yana kwance daga gefe yana nuna sama tare da yin murmushi an rubuta: “Ku cece ni daga auren da aka shirya.”

Kafar labarai ta Metro ta ruwaito cewa, matashin mai kirjire-kirkire ne kuma dan kasuwa ya kuma kafa kafar yanar gizo mai suna ‘findmalikawife.com’ da ke dauke da cikakkun bayanai kan niyyarsta neman masoyiya.

Da yake kare matakinsa, matashin mai shekara 29 ya ce, ya zama dole ne domin a gan shi kamar yadda ya gwada hanyoyin al’ada ba tare da wata yi fa’ida ba.

Mohammed ya ce: “Abokiyar zaman ta kasance mace mai kyau Musulma ’yar shekara 20, wacce take kokarin inganta
addininta.

“Kofa a bude take ga kowace kabila, amma ina da dangin da na fito na Punjabi mai karfi – amma ni kadai ne a wajen iyayena kuma ina kula da mahaifiyata da mahaifina. Idan ba a yarda da wannan yarjejeniya ba, ban
yi tsammanin matar za ta yi nasara ba.”

Matashin ya kara da cewa shi… siriri ne mai tsawon kafa 5 da inci 8, dan asalin birnin Landan, amma yana da wani
gida a Birmingham gidansa.

Godiya ga “mafi kyawun wuraren abinci a cikin gari, a Alum Rock da masallatai masu ban-sha’awa.”

Mutane sun mayar da martani shafukan sada zumunta inda wani mai adireshin: “@__shelann ya rubuta: “Yana iya ceton kansa idan masoyiyar ta shirya kanta
kamar yadda bangarorin biyu suka amince da hakan ya faru. !”